Ranar yaƙi da cutar Malaria | Labarai | DW | 25.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ranar yaƙi da cutar Malaria

Kamar yadda a ka sabba a rana mai kamar ta yau, wato 25 ga watan Aprul na ko wace shekara,Hukumar kulla da kiwon lahia ta Majalisar Ɗinkin Dunia, ta gayyaci gwamnatocin ƙasashen dunia, da ƙungiyoyi masu zaman kan su, su ƙaddamar da bikin faɗakarwa a game da illolin cutar massasara cizon sabro kokuma Malaria.

Ƙiddigar da hukumar WHO ko kuma OMS, ta gudanar, ta gano cewar a ko wace shekara, a ƙalla mutane milion 3 ke rasa rayuka a sabili da cutar Malaria, kuma kashi 90 bisa 100, a nahiyar Afrika.

Hukumar WHO,ta ce a duk tsukin rabin minti ɗaya, yaro ɗaya ke mutuwa dalili da cutar massara cizon sabro a nahiyar Afrika.

Rudolf Seiters, shine shugaban hukumar bada agaji ta Red Cross, a nan ƙasar Jamus ya yi ƙarin bayyani, a game da bala´in da cutar Malaria ke hadasawa a dunia.