1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar tunawa da kisan kiyashin da aka yiwa Yahudawa a Jamus

January 27, 2007
https://p.dw.com/p/BuTA

A dangane da bukin ranar tunawa da kisan kiyashin da aka yiwa Yahudawa a lokacin yakin duniya na biyu, SGJ Angela Merkel ta yi kira da karfafa yakin da ake yi da masu matsanancin ra´ayin nuna wariya. Merkel ta mika godiyarta ga dukkan masu fafatukar shimfida demukiradiya bisa gudunmawar da suke bayarwa. A yau ne a fadin tarayyar Jamus ake gudanar da bukukuwan tunawa da aukuwar kisan kare dangi da aka yiwa Yahudawa. Za´a yi shiru na wasu mintuna tare da ajiye furanni a sansanin gwale gwale na Ausschwitz, inda a ranar 27 ga watan janerun 1945, aka ceto wadanda ake tsare da su a can. Alkalumman sun yi nuni da cewa mutane kimanin miliyan 6 daukacin su Yahudawa aka kashe a zamanin mulkin ´yan NAZI.