Ranar tunawa da azabtad da jama′a a duniya. | Siyasa | DW | 26.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ranar tunawa da azabtad da jama'a a duniya.

Ranar 26 ga watan Yuni ne Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙaddamar, don tunawa da waɗanda ake gallaza wa a duniya baki ɗaya. Game da ayyukan da kwamitin kula da gallaza wa jama'a a duniya baki ɗaya ke yi ne, babbar sakatariyarsa Brita Sydhoff ta ba da ƙarin bayani.

Gallaza wa wani fursunan Iraqi da sojan Amirka ke yi a gidan yarin Abu Ghraib a Bagadaza.

Gallaza wa wani fursunan Iraqi da sojan Amirka ke yi a gidan yarin Abu Ghraib a Bagadaza.

Kwamitin ƙasa da ƙasa mai kula da waɗanda aka nuna wa azaba a duniya baki ɗaya, na da cibiyarsa ne a birnin Copenhagen na ƙasar Dennmark. Wata likitar ƙasar Sweden, Brita Sydhoff ce ke shugabancin kwamitin, tare da ma’aikata 27 a cibiyar. Sa’annan kuma, akwai reshen kwamitin a birnin Brussels, inda daga nan ne ake hulɗa da sauran kafofi a sassa daban-daban na duniya. Kwamitin dai na ƙoƙari ne, wajen tallafa wa waɗannan kafofin da shawarwari, da bayanai, sa’annan a wasu lokutan ma, da kuɗaɗe, idan yana da hanyar yin hakan. Babbar sakatariyar kwamitin, Brita Sydhoff, ta ce a ƙasashe masu ci gaban masana’antu, ana samun taimako kai tsaye daga gwamnatoci da hukumomi. Amma a wasu ƙasashen kuma, gwmanatocin ne ma ke da hannu wajen azabtad da jama’a, sabili da haka da wuya kuma, a ce su ne za su ba da kuɗaɗen yi musu jiyya ko kula da su. Babu dai yadda za a iya taimaka wa irin waɗannan mutanen, ba tare da isassun kuɗaɗe ba, inji jami’ar. Ta ƙara da cewa:-

„A halin yanzu dai, masu ba da tallafin kuɗi ga wannan fafutukar, su ne Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma Ƙungiyar EU. Ba don waɗannan kafofin guda biyu ba, da a ƙasashe da dama, inda har ila yau, ake azabtad da jama’a, ba za mu iya gudanad da ayyukanmu ba. Duk da hakan ma, muna huskantar matsaloli da dama, wajen tallafa wa takwarorinmu a wasu ƙasashen, saboda babu isassun kuɗaɗen yin hakan.“

Cibiyar kwamitin da ke birnin Copenhagen dai na tattara duk wasu labarun azabtad da jama’a ne daga sassa daban-daban na duniya. Sa’annan kuma, daga nan ne ake bai wa jami’an kiwon lafiya a ƙasashe daban-daban, bayanai kan hanyoyin yi wa waɗanda aka nuna wa azabar jiyya. Ban da haka kuma, cibiyar na tara labarai kan masu azabtarwar da kansu, don idan aka zo ga yi musu shari’a, a sami tabbataccen tushe na hujjoji. Game da tambayar ko kwamitin ya tara labarai kan Saddam Hussein, ko kuma ana amfani da waɗannan labaran a shari’ar da ake yi wa tsohon shugaban na Iraqi, Sydhoff ta bayyana cewa:-

„Ba na ganin zan iya ba da amsar wannan tambayar kai tsaye, duk da cewa, a Iraqin da wasu wurare ma, muna ƙoƙarin tattara hujjoji na gallaza wa jama’a da aka yi. A galibi, rashin cikakkun hujjoji ne ke sa ba a iya cafke waɗanda ake tuhuma da laifin gallaza wa jama’a don a gabatad da su gaban shari’a. Amma na san cewa, likitoci abokan aikina, a yankuna daban-daban na duniya na ƙoƙarin tattara irin waɗannan labaran, don a iya hukuntad da masu aikata laifuffukan.“

Maimakon a yi ta tara labarai dai, da zai fi inganci, a iya yin katsalandan, don hana gallaza wa jama’a a duk ƙasashen da ake tuhumar hakan zai iya aukuwa. A ran alhamis da ta wuce ne dai, ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya kan haramta azabtad da jama’a ya fara aiki. Tun shekara ta 2002 ne aka zartad da wannan ƙudurin, wanda ke bai wa jami’an Majalisar Ɗinkin Duniyar, damar kai ziyarar ba zato ba tsammani a gidajen yari, da tashoshin ’yan sanda da sansanonin ’yan gudun hijira, a duk ƙasashen da ake tuhumar cewa, wannan ɗanyen aikin na aukuwa a cikinsu. Bayan amincewa da yarjejeniyar da ƙasashen Boliviya da Honduras suka yi a ran 23 ga watan Mayu ne, aka sami yawan ƙasashe 20 da ake bukata, kafin ƙudurin ya fara aiki. Abin ban takaici ga ƙungiyoyin kare hakkin ɗan Adam, kamarsu Amnesty International, shi ne ganin cewa ƙasashe kamarsu Jamus ma, sun ƙi rattaba hannu kan yarjejeniyar.

  • Kwanan wata 26.06.2006
  • Mawallafi YAHAYA AHMED
  • Bugawa Buga wannan shafi
  • Permalink http://p.dw.com/p/Btzd
  • Kwanan wata 26.06.2006
  • Mawallafi YAHAYA AHMED
  • Bugawa Buga wannan shafi
  • Permalink http://p.dw.com/p/Btzd