1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Ranar tara ga watan nuwamba na da muhimmanci a tarihin Jamus

Tara ga watan Nuwamba a Jamus

default

Shugabar Gwamnati Angela Merkel

A yau 9 ga watan nuwamba aka yi bukin cika shekaru 18 da faduwar katangar Berlin, batun da ya canza duniya baki daya. Tun ba yi shekara daya ba wato a ranar 3 ga watan oktoban shekarar 1990 aka sake hade Jamus bayan shekaru 41 da raba ta. Karshen mulkin kama karya na hiyu a cikin Jamus wato rushewar JTG, ya goge mulkin gurguzu tsantsa daga taswirar siyasa ta Turai. Hakan ya kawo karshen yakin cacar baka tsakanin kasashen gabashi da na yammaci. 9 ga watan nuwanban shekarar 1989 ta kasance ranar da ta sauya makomar Jamus da Turai baki daya.

To sai dai ga tarihin Jamus ranar 9 ga watan nuwamba na da muhimmanci daban daban. A shekarar 1918 dan social democrat Philipp Scheidemann yayi shailar kafa janhuriyar Jamus. Hakan ya kawo karshen mulkin sarki sarakuna Wilhelm na biyu.

“Ma´aikata da sojoji na san ku san muhimmancin tarihin wannan rana. Wani abin al´ajabi ya faru. Jan aiki na gaban mu. Duka kuwa saboda jama´a ne. Ku hada kanku kuma ku san irin nauyin dake kanku. Mulkin mulukiya ya rushe. Yanzu sabuwar jamhuriyar Jamus ce aka kafa.”

Tun da farko fari dai jaririyar dimokuradiyya a Jamus ta yi ta fadi tashi. Masu neman sauyi da masu ra´ayin rikau sun yi ta kokarin kawad da ita. A ranar 9 ga watan nuwanban shekarar 1923 sojoji karkashin jagorancin Adolf Hitler sun kutsa cikin ofisoshin manyan hafsoshin sojin kasar. Sannan shekaru 10 baya Hitler ya karbi mulki a Jamus inda ya jefa duniya baki daya cikin wata akuba wato yakin duniya na biyu.

Tun daga sannan aka yi ta kwace kadarorin Yahudawa a Jamus kafin a shekarar 1942 a fara yi musu kisan kare dangi sannu a hankali. A ranr 9 ga watan nuwamban 1938 wato gabanin barkewar yakin duniya na biyu, an kona wuraren ibadar yahudawa tare da kwasar ganima a kantunansu a fadin Jamus. Sabanin ranar 9 ga watan nuwamban shekarar 1938, ranar 9 ga watan nuwamban shekarar 1989 aka ga faduwar katangar Berlin, abin da kawo wannan rana ba wanda yayi tunanin sa. Ba tare da bata lokaci ba kuwa aka bude kan iyakokin JTY ga al´umomin JTG. Watanni gabanin ranar an yi ta zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin jam´iyar gurguzu ta SED. Dubban ´yan JTG sun nemi mafaka a ofisoshin jakadancin JTY dake kasashen gabashin Turai. Bayan matsin lamba da suka sha hukumomin JTG sun sassauta dokokin hana fita waje ga ´yan kasar. Jim kadan bayan wannan sanarwa dubun dubatan mutane cikin doki da murna sun kwarara zuwa kan iyakokin tsakanin gabashin Berlin da Yammacin birnin, kamar yadda wannan dan JTG ya nunar.

“Da farko sun kyale mutane suna shiga daya bayan daya amma daga baya sun bude iyakokin gaba daya. Shi ya sa yanzu muna tsallakewa ba tare da nuna takardar shardar dan kasa ba. Ba´a caji ba na ma tare da wata takardar shaida.”

A dangane da abubuwan da suka faru a wannan dare, kowa ya san ba za´a koma ga tsohon zamanin baya ba. Faduwar wani sashe na bangon Berlin ya yi sanadiyar rushewar tsarin gurguzu a JTG. A karo na 4 ranar 9 ga watan nuwamba ta bar tarihi a Jamus, amma a wannan karo kyakkyawan tarihi.