Ranar Matasa mabiya darikar katolika na duniya | Zamantakewa | DW | 19.07.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Ranar Matasa mabiya darikar katolika na duniya

Paparoma Benedict na 16 ya nemi gafarar alúmar Australia game da lalata da kananan yara da wasu limaman chocin katolika suka aikata

default

Paparoma Benedict XVI ke jawabi ga taron matasa mabiya ɗarikar katolika.


A cigaba da taron matasa na duniya na mabiya ɗariƙar Katolika a ƙasar Australia, Paparoma Benedict na 16 nemi gafara game da tabargazar lalata da ƙananan yara da wasu limaman chocin suka aikata.


Paparoma Benedict ya nemi Afuwar ce yayin da yake jawabi ga dubban jamaá a wajen taron matasa na duniya na mabiya ɗariƙar katolika. Paparoman wanda ya nuna tausayin sa ga mutanen da wannan alámari ya shafa yayi amfani da wannan dama inda ya baiyana damuwa game da wannan abin kunya na cin mutunci ta hanyar lalata da limaman chocin katolika suka aikata akan ƙananan yara a wannan kasar ta Australia. "Yace yana mai matuƙar bada haƙuri ga ɓacin rai da baƙin ciki da mutanen da wannan abu ya shafa suke ciki". Ya kuma tabbatar musu da cewa a matsayi sa na jagoran su na addini yana tare da su a kowane hali.


Paparoma Benedict ya kuma yi kira ga Bishop - Bishop na ƙasar Australian su ɗauki dukkan matakan da suka wajaba domin hana aukuwar irin wannan ɗanyen aiki a nan gaba. Yana mai cewa wannan ya zubar da ƙima da martabar chocin na Katolika a idanun duniya. Ya kuma jaddada buƙatar adduoi na musamman ga yaran da aka yiwa wannan aika-aika domin tsarkake su daga wannan sabo.


Paparoman yace wannan mummunan rashin ɗaá da limaman suka aikata, cin amana ne ga amincewar da aka yi musu. yana mai tur da Allah wadai da wannan hali. Yace limaman sun jefa yaran cikin tsananin damuwa, a saboda haka yace wajibi ne a hukunta waɗanda suka aikata wannan ɓarna.


To sai dai a waje guda, ga ƙungyoyin dake kare haƙƙin yaran da limaman chocin suka ci zarafin su, sun ce neman gafara da Paparoman yayi bai wadatar ba. Hukumomi da ƙungiyoyi da iyalai da dama suna buƙatar Paparoman ya nemi yafewar su. A cewar wata ƙungiya mai suna Broken Rites, tace limaman chocin fiye da ɗari ɗaya ne suka aikata wannan laifi.


Babban limamin chocin Sydney Cardinal George Pell yace sun sami ƙararraki da dama daga mutanen da aka ci zarafin nasu. Kwanaki biyu gabanin ziyarar ta Paparoma zuwa Australia Cardinal Pell ya kafa kwamitin bincike domin bin diddigin waɗannan zarge zarge.


Babban taron matasan na duniya na bana na mabiya ɗariƙar katolika ya sami halartar matasa kimanin 500,000 waɗanda suka fito daga ƙasashe kimanin 170.