1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar mata

YAHAYA AHMEDNovember 24, 2005

Ran 25 ga watan Nuwamba ne ranar da aka kaddamar don nuna adawa ga addabar da ake yi wa mata a ko'ina a duniya. Alkaluma sun nuna cewa, a nan Jamus, ko wace mace daya cikin biyar na huskantar wannan illar.

https://p.dw.com/p/BvUH
Mata a Sin
Mata a SinHoto: AP

A ko’ina a duniya dai, a kan sami rahotannin gallaza wa mata da ake yi a ko yaushe. Ko a kasashe masu arzikin masana’antu ne, ko masu tasowa, babu inda wannan illar ba ta yaduwa. Kuma ba a cikin wani nau’i na musamman na al’umma ne ake samunta ba. A gidajen masu hannu da shuni, da na marsa abin hannunsu, duk akwai mazaje masu gallaza wa mata. A nan Jamus dai alkaluma na nuna cewa, ko wace mace daya cikin 5 na huskantar wannan matsalar. Kamar yadda Claudia Schrimpf, shugaban kungiyar „Frauen helfen Frauen“, wato kungiyar mata masu taimakar `yan uwansu mata, wadda ke da gini a unguwar Ehrenfeld da ke birnin Kolon, inda mata za su iya zuwa neman mafaka, ta bayyanar:-

„Ba duka kawai mata da dama da ke zuwa gunmu suke cewa an yi musu ba. Mazansu na kuma yi musu barazana, da hana su kudin kashewa, da dai makamancin haka. Wato ban da duka, akwai kuma hanyoyin da mazan ke bi suna nuna musu azaba.“

Har ila yau dai, a birnin Kolon, akwai kuma wani gida, wato „Elizabeth-Frey Haus“ na bai wa mata mafaka. Coci ne dai ke kula da su. A cikin shekara ta 2003 mata kusan dubu da dari 3 ne suka nemi mafaka a nan. Mafi yawansu kuwa, sun gudu ne saboda azabar da ake nuna musu a gidajen mazajensu ko kuma na iyayensu. Kahsi 30 cikin dari na wadannan matan, baki ne, wadanda a galibi suka fito daga Turkiyya, ko Rasha ko kuma Thailand. Wata mace mai suna Zhao, `yar kasar Sin, ita m ata taba neman mafaka a wannan gidan. Dalilin da ya sa ta yin haka kuwa, shi ne bayan wani dan rikici da suka samu da mijinta, sai ya fara dukanta, ba ya ba ta ko dari kuma na kashewa. Kai hatta kudin aikin sharar da take yi ma, sai mijin ya kwace daga hannunta. A wani lokacin ma, sai da ya yi niyyar shake ta, bayan ta ki ba shi dan karamin albashinta. Bayan ta iya ta kubuce masa, sai a tsorace, ta fice daga gidan. Amma da ta sami kanta a bakin titi, sai ta ga ba ta san inda za ta je ba kuma. Ga shi ita bakuwa ce a Kolon, ba ta iya yaren Jamusanci ba, kuma ba ta da kudi a hannunta. Sai yaya k Kamar yadda ta bayyanar:-

„Sai na yi ta tafiya dai haka nan a kan titi. Sa’ar da na ci, sai na gamu da wani dan sanda. Shi na ce ya taimake ni. Sai ya kai ni gidan bai wa mata mafaka. A nan na kwan, aka ba ni abinci. A nan ne kuma aka samar mini lauya. To kin ga sai na ji kamar a gidan uwata nake, babu abin da nake tsoro kuma.“

A nan Jamus dai, kananan hukumomi da coci-coci da kuma kungiyoyin sa kai da dama na samad da irin wadannan gidajen na bai wa matan da mazajensu ke nuna musu azaba a gidajensu mafaka. A galibi, idan matan suka yi kaura daga gidajensu, sai ka ga ba su da ko sisi a jikinsu, ba su kuma da mai taimakonsu.

To irin wadannan kafofin ne ke samar musu matsugunai na wucin gadi, su kuma nemar musu lauyoyi idan bukata ta kama, kamar dai alal misali batun Zhao daga kasar Sin. Idan kuma batun ya kai har kotu, su ma’aikatan kafofin ne ke raka matan zuwa gaban alkali.