1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Tunawa da ranar masu cutar sukari ko diabetes

Salissou Boukari
November 14, 2016

Likitoci a Nigeria sun bayyana muhimmancin yin gwaji a kai a kai don gano ko akwai ciwon sukari a jinin wadanda aka yi wa gwajin, da nufin daukan matakan shawo kansa da wuri a wani mataki na rigakafi.

https://p.dw.com/p/2SgTK
Deutschland Insulinspritze
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Kalaene

A kiyasi dai sama da mutum miliyan dari hudu da goma ne ked a ciwon sugar a duniya kuma Nigeria na daya daga cikin kasashen da lalurar ke kara yawa, wanda hakan ne ya sa kungiyar masu fama da ciwon sugar ke yawan  fadakar da jama’a muhimmancin yin gwaji don katse hanzarin tarin cututtukan da ke samun masu ciwon kamar yadda Dr Ibrahim D. Gezawa, babban likita a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano ya bayyana:

“Abin da ya kama daga samun mutuwar wani bangare na jiki da ake kira stroke a turance, zuwa makanta, haka kuma zuciya da hanyoyin jini kan iya samun heart attack wato bugawar zuciya ko mutuwar zuciya na lokaci daya.To haka hanyoyin  jinni da jijiyoyin  jinni da suke isar da sako su ma wadannan ciwon sugar yana yi musu illa. Iirin wadannan illollin hanyoyin  jinni da jijiyoyin jinni masu isar da sako, su ne suke haifar da yanayin yadda mutun ba zai dinga jin abu  a jikinsa ba ko kafa, haka kuma hannunsa idan ya taba abu ba zai sani ba. Wannan kuma zai haifar da yanayi na kamar wani ciwo haka ko kurji wanda nan da nan za ka  ga ya ci gaba da  mamaye kafar gaba daya yadda za a fara zancen yanke kafar.”

Deutschland Wunde offenes Bein
Hoto: picture-alliance/dpa/K. Rose

Akwai nau’o’in ciwon suga guda uku kuma nau’i na biyu wanda ya fi kama manya zuwa dattawa wanda a lokuta da dama  alamominsa basa bayyana har zuwa  lokacin da illoli daban-daban za su fara bujirowa. Dr Ibrahim ya yi karin haske kan abubuwan  da ke jawo nau’i na biyu na wannan ciwo:

“Na farko akwai rashin motsa jiki wanda shi rashin  motsa jiki a kwana a tashi zai haifar da da yanayi  na yadda insulin ba zai iya aikinsa yadda ya kamata ba. Sannan kuma zai iya haifar da kiba musamman idan ya hadu da ciye-ciye na kayayyaki ko abinci ko abin sha da ke dankare da ainihinkitse ko mai ko kuma zaki.”

Malam Yusuf Salisu Kura masani ne kan abincin masu lafiya da marasa lafiya a asibitin koyarwa na Aminu Kano, ya yi bayanin ire-irin abinci da mai ciwon suga zai rika ci don ya zauna lafiya.

Überfülltes Krankenhaus in China
Hoto: picture-alliance/dpa

“Misali dawa ko masara ko alkama ko gero ko taliya ko macroni.To duk wadanda  ake surfawa sai a gaya wa mai ciwon suga zai iya cin su amma babu surfe. A wanke a shanya sannan a nika lukui babu tankade. Da dusar ake so sai ka zo ka yi tuwon ka.Tuwo mara daya ka dau rabin mara idan ka cinye ba ka koshi ba sai ka yi kwadon ganye na zogale ko salat ko lamsir ka yi kwado ka ci ka koshi. Idan babu wannan  idan an sami data ko yalo ko gurji ko cucomba ka sa ka ci ka koshi ko yalon Bello ka ci ka koshi.”

Alamonin  cutar kamar yadda masana suka nuna, sun hada da yawon shan ruwa da futsari da bushewar makogoro da gani dishi dishi  sai kasala da rashin karfin mazakuta ga maza, ga mata kuma yawan bari ko haihuwar jarirai masu girma.