1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ranar majalisar dinkin duniya

A yau ake bikin ranar MDD ta duniya,inda kasashe membobi ke gudanar da taruka don kara ilamantar da jamaa aiyukan majalisar da manufar kafata a ranar 24 ga watan oktoba na 1945.

A jawabinsa wajen sakatare janar mai jiran gado na Ban Ki-Moon ya sanarda sabbin gyare gyare a cikin majalisar don maido da martabarta a idon duniya tare da kawo karshen rashin yarda da akeyiwa majalisar.

Ministan harkokin wajen na Koriya ta kudu wanda zai karbi ragamar shugabancin majalisar a ranar 1 ga watan janairu,yace babban abinda zai bada fifiko kansa shine,samun goyon bayan kasaahe a matsayinsa na sakatare janar.

A ranar 31 ga watabn disamba ne Kofi Annan zai sauka daga wannan mukami bayan sheakaru 5.