Ranar kare mahhali ta Majalisar Ɗinkin Dunia | Labarai | DW | 05.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ranar kare mahhali ta Majalisar Ɗinkin Dunia

Yau ne ranar da Majalisar Ɗinkin Dunia ta ware, domin yaƙi da gurɓacewar mahhali a dunia.

Ƙasashe daban-daban, sun yi anfani da wannan rana, domin faɗarkarwa, a game a da mattakan kare mahhali, da kuma illolin da ke tattare da taɓarɓarewar yanayi.

Albarkacin ranar komishinan zartsawa ta ƙungiyar gamayya turai, Stavros Dimas,yayi kira ga ƙasashen dunia, su himmantu, wajen neman hanyoyin rage ɗumamar yanayi, ta hanyar rage fidda gurɓatacen iskan gaz.

Ƙungiyar taraya Turai, ta buƙaci shugabanin G8, su yi anfani da damar taron da za su fara gobe, domin matsa ƙaimi, ga shugaban Georges Bush na Amurika, ya amince ya bada haɗin kai, ga yunƙurin ƙasashen dunia na yaƙi da ɗumamar yanayi.

A halin da ake ci dai, ƙasar Amurika, ta ƙi rattaba hannu, a kan yarjejeniyar Kyoto, wadda ta tanadi matakan yaƙi da gurɓatar yanayi.