1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka za ta fara amfani da harajin a kan bakin karfe

Abdourahamane Hassane
May 31, 2018

A gobe juma'a ne Amirka za ta soma yin aiki da sabbin haraji da ta saka a kan karfen gorar ruwa ko sanholama da kuma bakin karfe wanda ake shigo da shi daga kasashen Turai da Kanada da Mexiko zuwa Amirka.

https://p.dw.com/p/2yjVi
Aluminium-Produktion in China
Hoto: picture-alliance/dpa/Imaginechina

 Tuni da kungiyar tarrayar Turai ta yi watsi da harajin sannan kuma ta ce za ta kai kara a gaban babbar kungiyar kasuwanci ta duniya. Ita ma shugabar gwamnatin Jamus  Angela Merkel ta ce haraji na kudaden fito wanda ya wuce kima ya sabama kaida, ta kuma ce yin amfani da tsarin wani abu ne da zai dagula harkokin kasuwanci na duniya.