1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar Iyali ta MDD

May 15, 2007

A shekara ta 1993 ne MDD ta ware ranar 15 ga watan mayu domin zama ranar nuna zumunci ga iyali ta kasa da kasa

https://p.dw.com/p/Btva

A dai halin da ake ciki yanzun a nan Jamus kusan kashi daya bisa uku na yaran da ake haifa babu aure tsakanin iyayensu sannan kuma wasu yaran miliyan daya da rabi agola ne, wadanda iyayensu suka yi sabon aure, ko da yake akan fuskanci matsaloli wajen raba nauyin kula da yaran tsakanin ainifin iyayen nasu. Misali wani da ake kira Ingo Müller, wanda bayan rabuwa da matarsa yake kula da ‘yarsu akalla sau uku a mako. Ga dai abin da yake cewa lokacin da yake bayani game da haka:

“Ta kan kwana waje na sau daya a mako, sannan kashe gari in sake mayar da ita wajen uwarta. Sai kuma yammacin talata da kuma karshen mako.”

Ita tsofuwar matar dama ta taba aure tana kuma da da mai shekaru goma da haifuwa, wanda ya fadi albarkacin bakinsa yana mai cewar:

“To dai ubanninmu ba daya ba ne. Ni mahaifina sunansa Axel yana kuma zaune ne a Hamurg a yayinda ita Maeves sunan mahaifinta Ingo. Sai kuma Marx, wanda ake da cikinsa yanzu haka.”

Ita kanta mahaifiyar yaran Katja Engelbrecht tayi bayani a game da matsalolin da take fama dasu wajen tarbiyyar yara da kuma rudami da sukan shiga idan tayi batu a game da tsofon mijinta, inda kowane daga cikinsu kan yi zaton ko maganar babansa ake yi. Ta ce ba wai ita ce bata sha’awar zaman aure ta yadda za a samu kyakkyawar dangantaka tsakanin oba da uwa da ‘ya’yansu ba, amma abubuwa ne suka ta’azzara kuma zaman tarayya ya gagara tsakaninta da ubannin yaran. Sai dai kuma duk da wannan matsala, dukkan uabnnin na kaunar yaran basa nuna musu wariya in ji Katja Engelbrecht, wadda ta kara da cewar:

“Misali shi uban wannan yaron, yana kaunar ‘yata Jannis matuka da aniya, ya ma dauketa tamkar ‘yarsa ce ta ciki. Ya kan zo ya daukesu su biyu ya fita da su yawo ku zuwa cin abinci ba tare da wani banbanci ba.”

Wannan abu yana da muhimmanci dangane da tarbiyyar yara saboda kada su shiga zullumi su rika tunanin cewar babu mai sonsu a duniyar nan, saboda uwarsu ta rabu da mahaifinsu. Ingo Muüller dai ya ce da so samu ne da zai fi kaunar zama da iyalinsa saboda a ganinsa hakan shi ne mafi alheri ga rayuwar dan-Adam, cikin sukuni da kwanciyar hankali.