1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar fafutukar hana tilasa wa yara aikin soji.

February 11, 2006

Ranar 12 ga watan Farbariru ne aka kaddamar don nuna adawa ga salon tilasa wa yara shiga aikin soji a dole, musamman a yankunan da aka shafe shekaru da dama ana ta ke rikce-rikce.

https://p.dw.com/p/BvTp
Yara kanana dauke da makamai a yakin basasan kasar Laberiya.
Yara kanana dauke da makamai a yakin basasan kasar Laberiya.Hoto: dpa

A yankuna daban-daban na duniya inda ake yake-yake dai, ana lura da cewa, kamar yadda fafatawar ke dadewa haka kuma ake ta kara samun yara kanana a filin daga, wadanda ba da son su ne suke zuwa yakin ba. Kame su ake yi a tsoratad da su da azaba, sa’annan a tilasa musu daukan makamai zuwa bakin daga. Ana iya ganin hakan ne a zahiri, a yankunan da aka shafe shekaru da dama ana ta rikice-rikice, kamarsu Uganda, da Sudan da Côte d’Ivoire, da Kongo da Bama, da Phillipines, da Kolombiya da dai sauran wasu yankunan, inda yara kanana ke cikin rundunonin mayakan.

Don tsai da ci gaban wannan mummunan hali da kuma kawo karshensa ne, kungiyoyin sa kai da na kare hakkin dan Adam da dama a duniya suka hada gwiwa wajen daddage wa tilasa wa yara yin aikin soji. kungiyoyin dai sun kiyasci cewa, a duniya baki daya, kusan yara dubu dari 2 da 50 zuwa dubu dari 3 ne ke dauke da makamai a halin yanzu, kuma kusan kashi daya bisa uku na wannan adadin, `yan mata ne. Andreas Rister, wani jami’in kungiyar nan ta Terre des Hommes, daya daga cikin kungoyoyin da ke jagorancin wannan fafutukar, ya bayyana cewa:-

„Yaran da aka tilasa musu yin aikin soji dai, bas a samun damar cin moriyar yarantakansu. A cikin rukunai kalilan ne suke samun damar samun wani horo. Mafi yawansu ba su da ilimi na makaranta. Kazalika kuma, su ne kamuwa da yawan cututtuka su kuma huskanci matsalolin rayuwa a cikin jama’a. A duk tsawon rayuwarsu, bas u san komai ba sai bin oda irin na soji, inda tsoro ne kawai ya cika musu zukatansu. To irin wadannan yaran, idan an ceto su, matsalar da ake huskanta ita ce sake horad da su, don su fita daga wannan halin da suke ciki.“

Su dai masu tilasa wa yara shiga aikin sojin, a galibi, `yan kungiyoyin `yan tawaye ne, wadanda ko wane yaro suka samu mai shekaru daga 11 zuwa 17 da haihuwa ya dace musu. A wasu lokutan kuma, a kan sami irin wadannan yaran kuma a cikin rundunonin soji na hukuma. Mafi yawansu dai ana tilasa musu ne shiga aikin sojin. `Yan tawayen na iya kai farmaki a kan kauyuka don su sami yaran da za su iya tilasa wa daukan makamai, su shiga cikin rukuna mayakansu. To irin wannan farmakin ne ke tilasa wa jama’a da dama yin kaura da iyalansu daga matsugunansu zuwa manyan birane inda suke samun kansu cikin wasu munanan halaye, kamar yadda Andreas Rista ya ce halin da ake ciki ke nan yanzu a Colombiya:-

„Fiye da rabin jama’ar sun fada mana cewa, sun yi kaura ne saboda `yan tawayen sun zo kauyensu suka ce yaransu, da maza da mata, sun kai shekaru 11 zuwa 13. Sabila da haka, dole ne su dau makamai su shiga yaki. Ta hakan ne suke yin kaura zuwa Bogota, babban birnin kasar ta Colombiya. Amma a nan ma, suna samun kansu ne cikin wani mawuyacin hali na rayuwa. Duk da hakan, sun fi gwammacewa da wannan halin, maimakon su bari a dau waransu zuwa daji don yakin sunkuru.“

Ba duk iyalan ne ke samun damar kaurace wa `yan tawayen ba. A wasu lokutan su kann afka wa kauyukan ne ba zato ba tsammani, su kwashe yaran a cikin dare, su kai su wasu yankuna daban na kasar, ba tare da iyayensu sun san inda suke ba. Ba tare da wani horon aikin soji ba, ake tura su bakin daga, inda a galibi da yawa daga cikinsu ke halaka.

Wadanda suka sami damar kubuta daga hannun `yan tawayen, sai su kasance gas u nan ne dai, bas u san inda za su mai da alkibklar halin rayuwarsu ba. Suna kuma huskantar matsaloli wajen iya zama cikin jama’a.

Don tallafa wa irin wadannan yaran ne, aka kafa wasu cibiyoyin koyad da sana’o’i a kasar Laberiya, inda yaran da aka tilasa musu shiga soji a lokacin yakin basasan kasar, ke samun damar koyon sana’ar kafinta, da birikla, da dinki da gyara motoci da dai sauransu. To ta hakan ne dai kadan daga cikinsu ke iya samun aikin yi bayan horad da su da aka yi.

Kungiyar ta Terre des Hommes dai, ta yi kira ga gamayyar kasa da kasa da ta taimaka wajen ganin cewa, an aiwatad da ka’idojin yarjejeniyar da aka cim ma a Majalisar Dinkin Duniya, inda fiye da kasashe dari suka rattaba hannu kan wannan yarjejeniyar, wadda ta hana daukan duk yara masu kasa da shekaru 18 aikin soji. Ta hakan ne kawai, a ganin kungiyar, za a iya shawo kan wannan mummunan dabi’ar.