1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar cutar TB ta duniya

March 24, 2006

Mutane kimanin dubu biyar kan yi asarar rayukansu a kowace rana sakamakon cutar TB

https://p.dw.com/p/Bu11
Kwayoyin cutar TB
Kwayoyin cutar TBHoto: dpa

Cutar TB wata mummunar annoba ce da ta zama ruwan dare a duniya. Kuma ko da yake cutar na yaduwa a cikin gaggawa a nahiyar Afurka, amma ta fi addabar kasashen Asiya, wadanda ke da kashi 55 zuwa kashi 60% na illahirin masu fama da ita a duniya sai kuma kasashen Latin Amurka da na gabas ta Tsakiya da kuma kasashen gabacin Turai. An ji wannan bayanin ne daga Dr. Mario Raviglione darektan matakin kungiyar lafiya ta MDD WHO akan dakatar da yaduwar TB, wadda hatta kasashe mawadata dake da cin gaban masana’antu ba ta barsu ba. A hakika ana da ikon shawo kan wannan matsala tare da ceto rayukan mutanen dake fama da barazanar cutar in ji Bill Gates, wanda ya kirkiro Microsoft ta na’ura mai kwakwalwa, a lokacin da yake jawabi ga taron duniya akan tattalin arzikin da aka gudanar a Davos watan janairun da ya wuce, domin gabatar da matakinsa na yakar tarin fuka a duniya. Bill Gates ya kara da cewar:

2.O-Ton Gates

“Abin mamaki ne ganin yadda ake wa matsalar rikon sakainar kashi, musamman idan mutum ya lura da ci gaban fasahar dake akwai. Tun misalin shekaru dari da suka wuce ake da ikon gwada cutar tarin fuka. Amma an kasa inganta lambar riga kafinta da ba ta da tasiri. Har yau babu wani sabon maganin da aka kirkiro. Mataki mai tasirin da ake amfani da shi tun daga shekara ta 2000 shi ne na DOTS a takaice, wanda ya samu kyakkyawar nasara a kasashe da dama.”

Tun bayan gabatar da wannan mataki zuwa yanzu mutane miliyan 20 suka ci gajiyarsa. To sai dai kuma cutar ta TB ta kan dauki fasali ne iri daban-daban ta yadda ya zama wajibi a rika canza dabarun tinkararta in ji Dr. Mario Raviglione daga kungiyar lafiya ta MDD WHO, wanda ya kara da cewar:

3.O-Ton Raviglione

“Da farko wajibi ne a ba da la’akari da matsayin tsarin kiwon lafiya da kasashe ke dauka da kuma yadda suke tinkarar cutar ta TB. Dangane da kasashen dake da kwayar cutar mai taurin kai wajibi ne su samu wani maganin da ya banbanta da wanda aka saba amfani da shi yau da kullum a sauran kasashe. Akwai banbanci daga kasa zuwa kasa, amma a takaice shika-shikai biyar na matakin DOTS gama gari ne.”

An kiyasce cewar ana bukatar tsabar kudi dala miliyan dubu 56 wajen wanzar da shirin murkushe cutar ta tarin fuka a dukkan sassa na duniya a cikin shekaru 10 masu zuwa. A dai halin da ake ciki yanzu bankin duniya da gidauniyar Bill da Melinda-Gates sun yi alkawarin daukar nauyin dala miliyan dubu 25 daga wadannan kudade.