1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar buɗe ƙofofin masallatai ga waɗanda ba musulmi ba a Jamus

October 3, 2007
https://p.dw.com/p/Bu9c
A yau 3 ga watan oktoba masallatai kusan dubu 3 a nan Jamus sun bude kofofinsu ga mutane kimanin dubu 100 wadanda ba musulmi ba don kai ziyara a cikinsu. Bisa al´ada a kowace shekara a wannan rana ta bukin hadewar Jamus, shugabannin musulmi a Jamus kan ba wa wadanda ba musulmi ba damar kai ziyarar a masallatai a wani mataki na hade kawunan masu bin addinai daban daban. A yau din ne kuma Jamus ke bukin samun shekaru 17 da sake hade yankunan gabashi da yammacin kasar. A bana batun harajin nan da ake yiwa lakabi da harajin zumunci wanda ma´aikata ke biya don sake gina gabashin kasar ya fi dauki hankalin jama´a. Ana dai yawaita yin kira da a soke wannan haraji na kashi 5.5 cikin 100 na albashin kowane ma´aikaci a nan Jamus.