1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Ranar ƙananan yara ta duniya

Yau shekaru 18 kenan da zartas da ƙudurin kare ´yancin yara a duniya

default

Yara a Saliyo

A lokacin da ta ke da shekaru 17 an zubawa Hasina guba ta acid a fuska a ƙasar ta wato Bangladesh. Hakan ya faru ne bayan wata hatsaniya da ta yi da wani tsoho wanda ya ɗauki wannan mataki a kan ta, inda ya watsa mata gubar a fuska don ya ja kunnenta. Hasina zata ci-gaba da rayuwa da tabon da gubar ta bari har tsawon rayuwarta.

Hasina ta ce “A lokacin ina shirye shiryen halartar wani buki ne wanda da ni da ´yan´uwana muka daɗe muna begensa. Daddare lokacin da na ke barci bayan bukin sai na ji an zuba mun guba a fuska. Da farko ban san abin da ya faru ba. Na ji kamar ruwan zafi aka zuba min, amma sai na yi ta jin ƙuna na yi ta kara ina neman a ba ni ruwa amma ba a ba ni ba.”

Hasina wanda yanzu ta cika shekaru 20 ta samu taimako daga asusun taimakon yara na MƊD wato UNICEF. An yi mata aikin tiyata da yawa. A gun wani taro da asusun UNICEF ya shirya a birnin Berlin, a karon farko Hasina ta samu ƙwarin guiwar bayyana abin da ya farun. Mai kula da ´yancin ƙananan yara a Jamus Sabine Christiansen ta kaɗu da jin labarin Hasina. Ta ce abin takaici ne ganin yadda har yanzu ake cin zarafin ƙanana yara a duniya baki daya.

Alkalumman asusun UNICEF na nuni da cewa ana azabtar da miliyoyin yara ko yin lalata da su a duniya. Asusun ya ce ana bautar da yara kimanin miliyan 200 a duniya baki ɗaya yayin da a duk shekara masu fataucin bil Adama na sace yara miliyan daya da dubu 200. Hakan kuwa na faruwa ne duk da ƙkudurin kare ´yancin yara na MƊD wanda ƙasashen duniya suka sanyawa hannu.

Ko da yake matsalolin yara a Jamus ya banbanta to amma shugabar UNICEF a ƙasar Heide Simonis tsohuwar Firimiyar jihar Schleswig-Holstein ta yi suka da rashin daidata al´amura a kasashen masu arziki.

Simonis ta ce “Muna masu ra´ayin cewa a kasa kamar Jamus da ake da ƙarancin kananan yara, da zai fi kyau idan aka saka batun ´yancin yara a dokar kasa. Ana ina mai yin tuni da cewa Jamus ta sanya hannu kan ƙudurin MƊD na ba da kariya ga yara bisa wasu sharaddu. Muna kira da a dage sharuɗɗan. Majalisar dokoki ta sha yin magana a dangane da haka.”

Shi kuwa mai magana da yawon UNICEF Rudi Tarneden cewa ya yi an samu ingantuwa abubuwa da yawa sakamakon kudurin ´yancin yara na MDD.

Tarneden ya ce “Hakika ba a zayyana ci-gaban da ake samu a cikin wani kundi. To amma ƙudurin ya ba da gudunmawa alal misali a nan Jamus wajen bawa dukkan iyaye ´yancin renon yara bayan rabuwa. Wannan dai wani abu ne dake da alaka kai tsaye da ƙudurin.”Har yanzu ba a aiwatar da abubuwa da dama dake cikin kudurin kare ´yancin yara na MƊD ba alal misali yiwa dukkan jariri rajistar haihuwa kamar yadda kudurin ya nema. Rashin yin wannan rajista kuwa na janyo bacewar yara fiye da miliyan 50 a kowace shekara a duniya baki ɗaya.