Ranakkun bukukuwan na Majalisar Ɗunkin Duniya | Siyasa | DW | 06.01.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ranakkun bukukuwan na Majalisar Ɗunkin Duniya

Ƙasashen Duniya na amfani da matsayinsu a Majalisar wajen gabatar da manufofinsu

default

Cibiyar Majalisar a New York

Shekara ta 2010 data kama dai na ɗauke da alkawuran muhimman batutuwa da suka haɗar da zaɓen ƙasar Britania, wasan kwallon kafa ta duniya a Afrika ta kudu , da kuma kaddamar da sabon shirin hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka, dama wasu sabbin ranakku da Majalisar Ɗunkin Duniya ke shirin kaddamarwa.To sai dai shin menene tasirin wadannan ranakku ga al'umma da akeyi domin su?

"Watakila wannan shekara zata kasance ta yaki da yunwa da fata."

"Don Allah yi hakuri,ban san komai ba....."

shima wannan mutumin cewa yayi..

"Ban sani ba"

Ayayinda wannan matar tace..

"Watakila wanna shekarace ta tafiye-tafiye ko kuma tafiya gaba ɗaya?

"Dakata dakata wai ni ban sani ba.

A hukumance dai Majalisar Ɗunkin Duniya ta sanar da wannan shekarar a matsayin ta kusantar junan al'adu da kariya ga tsirrai. Batutuwa guda biyu da mutane bazasu iya bayanai akansu ba, duk da cewar an shiga shekarar ta 2010.

Matsalar a nan itace ba wai abubuwan sunyi wa mutane yawa har basa damuwa bane, sai dai ana iya cewa Majalisar Ɗunkin Duniya na kokarin inganta batutuwa masu yawa ne a lokaci guda. A bara kaɗai dai ta kaddamar da wasu sabbin ranakkun la'akari da wasu batutuwa guda uku, a bana kuma guda biyu, kuma a shekara ta 2011 zata gabatar da wasu biyu kokuma fiye da haka. Kuma hakan acewar masanin harkokin siyasa Johannes Varwick, sunyi yawa...

" Munga ƙaruwar yawan ranakkun gudanar da bukukuwa daban-daban, kuma idan aka gabatarwa da mutane abubuwa da yawa a lokaci guda, zasu rasa sanin me ake nufi da dukkanninsu"

Tun a shekarata 1957 nedai aka fara kaddamar da irin waɗannan ranakku da suka shafi abubuwa masu yawa. Daga nan ne kalandar Majalisar ta fara cika da ranakku bukukuwa. Inda yakai ga kusan kowace rana ana bukin wani abune na kasa da kasa.Ko meya haifar da hakan...Johannes Varwick yayi tsokaci...

"Hakan nada nasabar cewar, akwai wasu kasashe dake da wakilci a majalisar , dake neman biyan bukatunsu.kuma babu wanda ya isa ya kalubalanci irin wadannan kasashe. Idan da alal misali ina zauren mashawartar Majalisar sa'annan wata kasa tace tana so ayi bukin ranar dankali ta duniya,watakila nima da zan amince.Bawai suna musgunawa kowa bane, sai dai kawai sukanyi yawa ne, wasu kuma babu ma'ana ballantana yin wani tasiri"

Watakila a Majalisar ta hango waɗannan matsaloli ne a shekara ta 1980. Kamar yadda Babbar Direktar ƙungiyar kyautata dangantakar Jamus da Majalisar Ɗunkin Duniya Beate Wagner ta nuna dacewar, a wannan lokaci ne zauren mashawartar majalisar ta zartar da kudurin dake la'akari da zaɓen batutuwan da za'a rika bukukuwa akansu.

"Su kasance suna da alaka da kudurori da manufofin Majalisar Ɗunkin Duniya, kuma ya kasance mafi yawan kasashe masu wakilci suna da ra'ayi akan kowane batu, kuma ya kasance akwai ɗan giɓi ko tazara tsakanin wata shekara da wata, ba wai kowace shekarace za a gabatar a matsayin shekarar....."

To sai dai bayan wannan ƙuduri, bisa dukkan alamu wannan majalisa dake zama uwa ma bada mama wa kasashen Duniya ta kama hanyar kaucewa manufofinta, wanda kuma hakan babban kuskure ne.Domin duk dacewar Zauren mashawartar Majalisar Ɗunkin Duniya ne keda alhakin sanar da irin waɗannan ranakku,sukanyi dogaro ne akan gwamnatoci da ƙungiyoyi masu zaman kansu, da na al'umma domin tabbatar da su.

Mawallafa: Zainab Mohammed/Walker Tamsim

Edita: Ahmad Tijani Lawal