Rana ta karshe a taron kolin kasashen kungiyar APEC | Labarai | DW | 19.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rana ta karshe a taron kolin kasashen kungiyar APEC

Shugabannin kasashen kungiyar habaka tattalin arzikin yankin Asiya da Pacifik sun sake hallara a birnin Busan na kasar KTK a rana ta biyu kuma ta karshe a taron kolin kungiyar ta APEC. Batutuwan cinikaiyar duniya, ayyukan ta´addanci da kuma barazanar annobar masassarar tsuntsaye su ne suka mamaye taron da shugabannin 21 na kasashen kungiyar ta APEC ke yi. Ana sa ran cewa shugabannin zasu fid da wata sanarwa wadda zata yi kira karara game da samun wani ci-gaba a taron da kungiyar cinikaiya ta duniya zata yi a Hongkong a cikin watan desamba. An dai yi arangama tsakanin ´yan sandan kwantar da tarzoma da masu zanga zanga a rana ta farko ta taron kolin.