Rana ta karshe a taron kolin Afirka da Faransa a Bamako | Labarai | DW | 04.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rana ta karshe a taron kolin Afirka da Faransa a Bamako

Shawarwari akan matsalolin nahiyar Afirka da su kama daga yake yake da nuna adalaci a huldar cinikaiya zuwa matsalar bakin haure zasu dabaibaye rana ta biyu kuma ta karshe a taron koli tsakanin shugaban Faransa Jaques Chirac da takwarorinsa na Afirka a yau lahadi. Shugaba Chirac da wasu shugabannin Afirka fiye da 20 na gudanar da taron ne a Bamako babban birnin kasar Mali, don tattaunawa akan taron cinikaiya kasa da kasa da zai gudana a Hongkong a a cikin watannan na desamba. Bukatar yiwa kasashe matalauta adalci a huldar cinikaiyar duniya na daya daga cikin muhimman batutuwan da aka mayar da hankali akai a rana ta farkon ta taron kolin na birnin Bamako. Taron kungiyar cinikaiya ta duniya da za´a fara a ranar 13 ga wannan wata zai kimanta shawarwarin birnin Doha da aka kaddamar a cikin shekara ta 2001.