Rana ta farko na jifan Shaiɗan a yayin aikin hajji | Labarai | DW | 19.12.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rana ta farko na jifan Shaiɗan a yayin aikin hajji

A rana ta uku da shiga aikin hajji,Alumomin musulmi da suka samu sukunin sauke farali na wannan shekara a kasa mai tsarki na cigaba da jifan shaidan a yau a wajen garin Mekka,bayan aske kawunan su tare da sayen ragunan layya.Da yawa daga cikin su dai sun iso wurin jifan ne da kunburarrun kafafu ,bayan tafiyar kimanin km 20 cikin dare daga Arafat,tare da kajeren hutu na saoi da barci a kewayen Musdalifa,inda nan ne suka tsinci duwatsu akalla 49, kowane mutum guda.

A sauran kasashen duniya kuwa Alkummar musulmi na cigaba da gudanar da shagulgulan sallar Layya,tare da gudanar da bukukuwan murna dake tattare da kewayowar wannan rana,kuma Allah ya maimaita mana.

 • Kwanan wata 19.12.2007
 • Mawallafi Zainab Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Cds0
 • Kwanan wata 19.12.2007
 • Mawallafi Zainab Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Cds0