1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rana ta biyu a ziiyarar da shugaban kasar Jamus ya kai Ghana

Shugaban kasar Jamus Hörst Köhler, ya shiga rana ta biyu aci gaba da ziyarar aiki daya kai izuwa Ghana.

Jim kadan bayan tattaunawar su da shugaba John Kufor na Ghana, shugaban na Jamusawa ya bukaci kasashen Afrika dasu karfafa dangantaka da takwarorin su na nahiyar turai a fannoni daban daban na rayuwa.

A dai wani lokaci ne a yau, ake sa ran Mr Köhler zai halarci wani taron karfafa dangantaka, a tsakanin kasashen nahiyoyin biyu a babban birnin kasar wato Accra.