1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rana ta biyu a taron kolin tarayyar Turai akan kasafin kudin ta

Mohammad Nasiru AwalDecember 16, 2005

Shugabannin kungiyar EU na fatan cimma wata yarjejeniya a gun taron koli na birnin Brussels

https://p.dw.com/p/Bu3L
Schüssel da Barroso da Merkel a Brussels
Schüssel da Barroso da Merkel a BrusselsHoto: AP

Tare da sara ana duban bakin gatari an nuna kyakkyawan fata a karshen rana ta farko a taron kolin KTT akan kasafin kudin kungiyar daga shekara ta 2007 zuwa ta 2013 da kuma batun rangwamin da ake yiwa Birtaniya. Da farko dai Birtaniya mai rike da shugabancin EU a yanzu ta ba da shawarar rage wannan rangwami da kimanin Euro miliyan dubu 8. To amma daukacin mahalarta taron sun yi watsi da wannan tayi da cewa yayi kadan. Amma yanzu ana fatan cimma daidato a yau juma´a rana ta biyu ta taron kolin na birni Brussels, inji FM Sweden Goran Persson.

“Ban yi mamakin ganni yadda tattaunawar akan kasafin kudin ta yi zafi ba. An fuskanci bambamcin ra´ayi, amma duk da haka mun kwana da sanin cewa idan ba mu cimma yarjejeniya yanzu ba, to a badi ma ba za´a samu wani ci-gaba ba. Ana tsammanin da akwai damar cimma wata yarjejeniya.”

Shi ma shugaban hukumar zartaswar EU Jose Manuel Barroso yayi fatan cimma wata masalaha bisa sharadin cewa Birtaniya zata yi sassauci.

“Na yi imanin cewa za su gabatar da wata sabuwar shawara wadda na ke gani zata sauya matsayin Birtaniya.”

Su ma a nasu bangaren shugabannin gwamnatoci masu ra´ayin mazan jiya da masu sassaucin ra´ayin daga cikin kasashen kungiyar ta EU da suka gana jim kadan gabanin taron kolin sun yi kira ga Tony Blair da ya yiwa shawawarin da ya gabatar gyaran fuska, kamar yadda SGJ Angela Merkel ta nunar.

“Zamu yi nazari sosai kafin mu shiga zauren taro. Jamus ba zata amince da kowace yarjejeniya ko ta halin kaka ba.”

Merkel ta je Brussels din ne tana mai mayar da hankali akan talafin da ake ba jihohin gabashin Jamus. Ta bayyana shawarar da Birtaniya ta gabatar ta tara sama da euro miliyan dubu 13 kafin shekara ta 2013 da cewa ba ta wadatar ba. Ta ce rage kasafin kudin kungiyar EU kamar yadda Birtaniya take nema zai fi shafar sabbin kasashen kungiyar. A halin da ake ciki kasar Poland ta yi barazanar hawa kujerar naki don kalubalantar shawarar ta Birtaniya. Yayin da ita kuma Faransa kamar farko ke goyon bayan ci-gaba da ba da makudan kudaden tallafi ga manoma, wanda kasar ta fi cin gajiyarsa.

Kamar dai kullum ana samun sabanin ra´ayi tsakanin manufofin kasa da kuma manufofin bai daya na kungiyar ta EU. FM Birtaniya Tony Blair ya tabo wannan batu yana mai cewa.

“Bisa ka´ida kowa na son a cimma wata yarjejeniya, amma a aikace kowa na da manufar da yake bi.”

Tattaunawar ta yau juma´a zata nuna irin alkiblar da za´a fuskanta wato ko za´a cimma daidaito ko a´a.