1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rana ta biyu a taron kolin kungiyar tarayyar Turai a Brussels

December 16, 2005
https://p.dw.com/p/BvGF

A yau ne ake shiga rana ta biyu a taron kolin shugabannin kasashen KTT a Brussels da nufin warware takaddamar da ake yi dangane da kasafin kudin kungiyar daga shekara ta 2007 zuwa ta 2013. Bayan tattaunawar da aka yi a rana ta farko an jiyo FM Birtaniya Tony Blair na cewa shugabannin kungiyar ta EU sun amince cewar dole ne a cimma wata masalaha akan wannan batu. Shugaban hukumar kungiyar EU Jose Manuel Barroso ya ce ko da yake har yanzu akwai sabanin ra´ayoyi, amma a yau FM Blair zai gabatar da sabbin shawarwari bisa manufar gano bakin zaren warware batun rangwamin da ake yiwa Birtaniya na biya kudin gudummawa ga EU. Rashin cimma daidaito akan batun kasafin kudin ka iya jefa kungiyar ta EU cikin wani mawuyacin hali na kudi wanda hakan zai yi barazana ga manufar wanzuwar tarayyar Turan. Wasu batutuwa dake daukar hankali a zauren taron sun hada da taimakon da ake ba kasashen gabashin Turai membobin kungiyar sai kuma batun manufar aikin gona ta bai daya.