1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ramatu Inuwa Yakasai

Al'amarin fatauci da miyagun kwayoyi da sauran abubuwan ta'asa ya jawo bacin sunnan Nigeriya wanda ke kokarin yada kimar ta.
Tun daga lokacin da ya hau mulki shugaban Nigeriya Olusegun Obasanjo yayi kokarin ganin ya kakkabe irin wannan hali dake neman mayar da kasar baya,amma kuma an kafa sabuwar doka kann haramtattun kudi cikin watan mayu, makon daya wuce ne hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Nigeriya ta fara wayar da kai dangane da wannan doka yayin wata bita a' lagos.Mataimakin shugaban Nigeriya Atiku Abubkar ne ya bude bitar,yayin bude butar yayi bayanin cewa, irin wannan kudi sun zama abin kyama a' Nigeriya mussanman ma idna a'kayi la'akari da yadda irin wannan hanyoyi ke tarnaki dga kimar kasar. Kamar yadda mataimakin shugaban kasar ta Nigeeriya ya fada yaki da fataucin miyagun kwayoyi da kasar ta shiga yi ya taimakawa kwarai kodayake kuma akwai bukatar kara tashi tsaye ko kasar ta fidda kanta da ga irin wannan kudaddde abin kyama, yace, tsarin ya haddarda tura haramtattaun kudadde daga kasashen waje zuwa bankunnan Nigeriya dan badda kamannin a'salin kudadden wanda idan a'ka bincika sai a' gano cewa, an samo irin wannan kudadde ne ta hanyoyin ta'asa ko kuma fataucin miyagun kwayoyi da wasu kulla kulla da suka kauyewa hanya ta halal ciki harda hanyar zamba ta 419. Yana da wahalar gaske a' iya sanin ainihin a'dadin kudadden da ke shiga cikin kasar irin wannan inji John Ndukuba wani lauya dake taimakwa wajen farke layar yan'419,yace kudadden kann kai kamar biliyoyin dala kuma da wuya kaga wadanda irin wannan matsala ta zamba ta rutsa dasu sun kai rahoto ga yan' sanda kuma ma koda sun je din da wuya kaga sun iya bayyana ainihin irin a'sarar da suka yi. Wannan bayani nasa yazo kusa da na mukadashin darektan hukumar ta yaki da fatauci da miyagun kwayoyi Jonah Achema dayace, abin da yake sanyawa gaba daya a' gaza hakikance ainihin a'dadin irin wannan haramtattun kudadde da a'ke mayarwa halatattu shine yawan su daya zarce hankali kudin sun haddarda waddanda a'ka samu daga hanyoyin kwayoyi cin hanci da rashawa da ciniki na mata masu zaman kansu da kuma kin biyan kudadden haraji da almubazzaranci.Kokarin da Nigeriya ta shiga yi nada nasaba da wani kwamitin da hukumar nan ta Geneva ta kafa karkashin laimar majalisar dinkin duniya dangane da hallata harmatattaun kudadde, bayan da Nigeriya ta tsallake rijiya baya inda a' shekarar data wuce shugaban na Nigeriya ya sanya hannu kann wasu doka guda uku kafin wa'adin wannan hukumar ta Geneva ta cika. Wannan doka da a'ka kafa cikin shekarar 1995 da ta dubu biyu da uku ta bukaci bankuna su bada rahoton duk wasu kudadden da a'ka ajiye a' gurin su da ya wuce dala dubu goma.Mathew Agbogun wani jami'in majalisar kula da harkokin fitar da kayayyaki daga Nigeriya ya yaba da kokarin gwamnatin ta Nigeriya na kakakbe irin wannan al'amari