Rahoton shekara - shekara na Unicef a game da rayuwar yara kanana | Labarai | DW | 14.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rahoton shekara - shekara na Unicef a game da rayuwar yara kanana

Yau ne hukumar majalisar Dinkin Dunia, mai kullla da yara kanana, wato UNICEF ta hiddo rahoton ta ,na shekara shekara.

Rahoton ya ce kasashe masu arzikin masana´antu na ci gaba da wa matsalar milliyoyin kanana yara a dunia daukar sakainan kashi.

Idan a ka yi la´akari da burin majalisar Majaliosar Dinki Dunia na rage talaulaci a dunia nan da shekarau 10 masu zuwa ta hanyar fadada illimi da mattakan kiwon lahia to har yanzu akawi sauran rina kaba , inji daraktan hukumar Unicef Madame Ann Veneman.

Yaki da talauci ya ta´alaka da halin da yara manyan gobe, ke ciki , to saidai abun takaici, yanayin halin a yanzu na da matukar muni.

Duk da cewar an samu ci gaba ahanyoyin dabandabnan , a shekara banna daruruwan miliyoyin kanannyara inni rahoto na Unicef su ka shekara cikin halin bala´in yinwa, da kunci rayuwa iri daban daban.

Alal misali, a ko wannan minti daya, yaro daya, dan kasa da shekaru 15, ke mutuwa da cutar Aids, wani dayan kuma, ke kamuwa da ita.

Kazalika, ko wanne minti daya,daya daga yara yan tsakanin shekaru,15 zuwa 24 a dunia, ke kamuwa da cutar Sida.

Kungiyar Unicef ta kira domin kara daukar matakan kulla da yara kanana.