Rahoton shekara shekara na komitin kare hakkokin yan jarida na dunia
February 14, 2006Komitin kare hakokin yan jarida na dunia, wato CPJ, ya bayyana rahoton sa na shekara ta 2005, a game da halin da yan jarida su ka gudanar da ayyuka.
A sakamokon wannan rahoto komitin yace an samu ci gaban mai ginan rijiya, ta fannin ayyukan jarida a kasashen daban daban na dunia.
Daga Latin Amurika, zuwa yankin gabas ta tsakiya,da wasu sassa na Afrika, ya jarida sun ga azaba, a shekara da ta gabata.
A jimilce, yan jarida 47 su ka rasa rayuka, a cikin aiki a tsawan shekara.
Sannan ga Karin wasu 22, da su ka mutu, daga farkon shekara banna kawo yanzu.
Idan a ka hada da shekara ta 2004, baki daya yan jarida, fiye da 100 su ka mutu cikin aiki.
Wannan su ne alkallumma mafi yawa, a tsawan shekaru 10, da su ka wuce.
Fiye da kashi 3 bisa 4, na wannan yan jarida, an kashe su, ta hanyar shirya masu ta´adanci, kuma ya zuwa yanzu, ba a hukunta wanda su ka shirya wannan kissa ba.
Ta bangaren yan jaridar da a ka kulle,baki daya addadin su, ya tashi 125 a kasashe 24 na dunia.