1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton shekara shekara na ƙungiyar kare haƙƙoƙin yan jarida ta dunia IPI

March 30, 2006
https://p.dw.com/p/Bv3f

A sahiyar yau ne a birnin Vienna,ƙungiyar kare haƙƙoƙin yan jarida da dunia, wato IPI, ta bayyana rahoton ta na shekara da ta gabata.

Rahotion yace, a shekara ta 2005, baki ɗaya yan jarida 65 su ka rasa rayuka, a bakin aiki, a ƙasashe daban daban na dunia.

Ƙasar Irak ke sahun gaba, daga jerin ƙasashe 175 da ƙungiyar ta gudanar da bincike.

A wannan ƙasa, yan neman rahoto 23 su ka riga mu gidan gaskiya, a shekara ta 2005.

Sannan 9 a ƙasar Phillipines, 3 a Bangladesh, da Haiti sai kuma, yan jarida 27, a cikin sauran wasu ƙasashe 18.

Bayan mace-mace, da ake samu a cikin wannan aiki, rahoton ya bayana ƙaruwar barazana, da tauye haƙƙoƙi da yan jaridar ke fuskanta, daga gwamnatoci, da ma wasu jama´a.

Mussamman ƙungiyar IPI, ta yi suka da kakkausar harshe ga ƙasar China, wadda ta yi ƙaurin suna ta wannan fanni.

An girka IPI, tun shekara ta 1950 a ƙasar Amurika, kuma a halin da a ke ciki, ta na da rassa, a ƙasashe 120 na dunia.