Rahoton Shekara Na UNICEF | Siyasa | DW | 10.05.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rahoton Shekara Na UNICEF

Kananan yara da matasa a sassa dabam-dabam na duniya ke dada fadawa cikin mawuyacin hali na rashin sanin tabbas game da makomarsu sakamakon yunwa da talauci da su kan sha famar fuskanta a rayuwarsu ta yau da kullum, ba kuwa a kasashen da ake fama da rikici a cikinsu kadai ba, a cewar asusun taimakon yara na MDD UNICEF

Hali da yara ke ciki a Bujumbura, fadar mulkin kasar Burundi

Hali da yara ke ciki a Bujumbura, fadar mulkin kasar Burundi

A cikin rahotonsa na shekara asusun taimakon yara na MDD UNICEF yayi kokarin janyo hankali ne ga mawuyacin halin da ake ciki a yankunan da ake fama da rikice-rikice a cikinsu. Domin kuwa a yayinda duniya baki daya aka mayar da hankali ga halin da ake ciki a kasashen Iraki da Afghanistan, akwai miliyoyin yara dake fama da ciwarwaci da karancin abinci mai gina jiki a sauran sassan da aka yi watsi da makomarsu, kamar dai kasashen Angola da Somaliya da kuma Sudan. A lokacin da yake bayani a game da mawucin halin da ake ciki, Dietrich Garlichs mai kula da al’amuran asusun UNICEF cewa yayi:

A kasashe goma daga cikin kasashen da lamarin ya shafa, yara miliyan daya da dubu dari biyar suka yi asarar rayukansu sakamakon karancin abinci mai gina jiki da ruwan sha mai tsafta da kuma tabarbarewar al’amuran kiwon lafiya. A kasar Kongo, alal-misali yara dubu dari biyar dake kasa da shekaru biyar na haifuwa suka yi asarar rayukansu shekarar da ta wuce, a yayinda adadin ya kama na yara dubu metan a Angola sai kuma wasu sama da dubu dari a Somaliya.

Yawa-yawancin cututtukan dake halaka yaran sun hada da kyanda da gudawa sai kuma mura, wacce ta kan halaka su sakamakon karancin abinci mai gina jiki da suke fama da shi, inda su kan wayi gari ba su da koshin lafiya. A halin da ake ciki yanzu lamarin ya fi yin tsamari a yammacin kasar Sudan, inda mutane sama da miliyan daya ke kan hanyarsu ta gudun hijira. Sojojin gwamnati da dakarun sa kai na daukar matakan keta haddin dan-Adam kuma babu wata takamaimiyar kafa ta kai taimakon jinkai zuwa yankin a cewar Rudi Tarneden, kakakin reshen asusun UNICEF a nan Jamus. Ya kuma kara da cewar:

Matsalar dake akwai ita ce ta karancin abinci mai gina jiki, inda rahotanni suka ce a wasu sansanonin na ‚yan gudun hijira kimanin kashi 80% na yaran ne ke fama da wannan matsala. Akan lura da hakan ne sakamakon wasu cututtuka na fata da kan bayyana a jikinsu da kwantsa a idanuwa da kuma hali na zullumi da suke ciki.

Ita ma kasar Georgiya tana daga cikin yankunan dake fama da rikici, duk kuwa da canjin mulkin da aka samu a cikin ruwan sanyi a kasar. Kimanin yara da matasa dubu dari uku ke bukatar taimako na kiwon lafiya da makarantu, lamarin da ya ta’azzara sakamakon karancin kudi da asusun UNICEF ke fama da shi. A sabili da haka Harry Lafontane, jakadan asusun yake gabatar da kira ga wadanda alhakin al’amurra ya rataya wuyansu da su yi watsi da manufofinsu na son kai su mayar da hankali ga makomar yara. A shekarar da ta gabata asusun ya fuskanci gibin kusan dala miliyan 200, wanda ya kama kwatankwacin kashi 40% na kasafin kudinsa.