Rahoton shekara na kungiyar taimako ta mujami′ar katolika Misereor dake nan Jamus | Siyasa | DW | 06.07.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rahoton shekara na kungiyar taimako ta mujami'ar katolika Misereor dake nan Jamus

A cikin rahotonta na shekara kungiyar taimako ta Misereor tayi korafi a game da yadda gwamnatocin kasashe masu ci gaban masana'antu suke wa manufofin taimakon raya kasashe masu tasowa rikon sakainar kashi

Kungiyar ta Misereor da Cibiyar Taimakon Kasashe Masu Tasowa ta mujami’ar Katolika sun lura da wani dan ci gaba da aka samu shekarar da ta wuce. Kungiyar ta ce ta samu karin yawan kudadenta na taimako da misalin kashi 2.5% sakamakon gudummawar da ta samu daga jama’a. Ita ma Cibiyar Katolikar ta KZE a takaice ta samu bunkasar yawan kudaden da ma’aikatar taimakon raya kasashe masu tasowa ta Jamus ta saba ware mata daga Euro miliyan 91 a shekara ta 2002 zuwa Euro miliyan dubu 94 shekarar da ta wuce. Amma duk da wannan bunkasar kungiyoyin biyu sun bayyana takaicinsu a game da koma bayan da ake fama da shi a manufofin taimakon raya kasashe masu tasowa. A lokacin da yake bayani game da haka darektan kungiyar Misereor Josef Sayer ya nuna rashin gamsuwarsa a game da bayanin da sakatare-janar na MDD Kofi Annan ya bayar na cewar majalisar zata cimma burinta na kayyade yawan ‚yan rabbana ka wadata mu da misalin kashi 50% nan da shekara ta 2015. Wannan ci gaban ya shafi kasashen China da Indiya ne kawai, wadanda suka fi yawan jama’a a duniya. Amma a baya ga haka za a ci gaba da fama da matsalar yunwa dangane da mutane miliyan 400 da kuma wasu da zasu kasance cikin dimuwa ta talauci su kimanin miliyan 600. Wannan mummunar tabargaza ce ta la’akari da dimbim arzikin da Allah Ya fuwa ce wa duniyar baki daya. Kungiyoyin guda biyu na Misereor da KZE sun, kazalika, sun bayyana takaicinsu a game da rashin wani takamaiman ci gaban da ake samu dangane da matakan yaki da cutar Aids da mace-macen yara kanana da samar da ruwan sha mai tsafta ga mutane. Wannan matsalar ta fi addabar yankin kudancin Afurka inda babu wata alamar dake nuna cewar za a cimma manufar da aka tanadar dangane da shekara ta 2015, sai dai fa idan an samu sauyi ga manufofin na kasa da kasa domin raya kasashe masu tasowa. Wani mummunan ci gaba kuma da kungiyoyin biyu suka lura da shi shi ne sabuwar alkiblar da aka fuskanta na ba da fifiko ga matakan soja da ake yi da sunan yaki da ayyukan ta’addanci sakamakon tsautsayin nan na sha daya ga watan satumban shekara ta 2001. Manufofin taimakon raya kasashe masu tasowa gaba daya suna fuskantar barazanar komawa wasu manufofi na soja, a cewar Josef Sayer darektan kungiyar Misereor ta mujami’ar Katolika. Yawa-yawanci akan yi amfani da ainifin kudaden da aka kasafta domin taimakon raya kasa ne wajen tafiyar da wadannan matakai. Kungiyar ba ta dadara ba tana mai korafi a game da rikon sakainar kashin da gwamnatin Jamus ke wa manufofinta na taimakon raya kasashe masu tasowa, inda har yau ta kasa cika alkawarin da tayi na bunkasa yawan kudaden taimakon domin su kama kashi sifiliu da digo 33% na jumullar abin da kasar ke samarwa a shekara. Kakakin cibiyar taimakon raya kasashe masu tasowa ta mujami’ar Katolika Karl Jüsten ya ce cibiyar tasa ba zata saduda ba zata ci gaba da matsin kaimi wajen ganin lalle gwamnati tayi kari akan abin da ta saba kasaftawa na taimakon kasashe masu tasowa duk da matakai na tsumulmular kudi da take dauka.