Rahoton Shekara Na Kungiyar Likitoci Ta Duniya | Siyasa | DW | 16.07.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rahoton Shekara Na Kungiyar Likitoci Ta Duniya

A cikin rahotonta na shekara kungiyar likitoci ta kasa da kasa tayi gargadi a game da yiwuwar billar wasu cututtuka a Darfur ta kasar Sudan

A dai halin da ake ciki yanzun kungiyar taimako ta likitoci ta fi mayar da hankalinta ne akan kasar Sudan, inda take da jami’anta kimanin 120 a lardin Darfur da kuma sansanonin ‚yan gudun hijirar kasar ta Sudan a Chadi. Duka-duka ‚yan gudun hijira dubu 400 ne kawai kungiyar ke da ikon kai musu taimakon magunguna. A lokacin da take bayani game da haka wakiliyar kungiyar a nan Jamus Ulrike von Pilar tayi korafin cewar gwamnatin Sudan, a bangare guda ita ce ummal’aba’isin wannan mawuyacin halin da aka shiga saboda kin ba wa kungiyoyin taimako na kasa da kasa damar kai dauki ga mutanen da matsalar ta shafa, sannan a daya bangaren kuna kafofi na kasa da kasa kamar MDD suna da rabonsu na alhaki saboda dadewar da suka yi suna wa matsalar rikon sakainar kashi. A halin yanzu haka ‚yan gudun hijira na fama da karancin abinci da ruwan sha mai tsafta kuma a halin yanzu haka ana hangen karatowar damina, wacce zata haifar da wata sabuwar matsalar. Da zarar daminar ta kama za a shiga hali na kaka-nika-yi saboda barazanar fuskantar yaduwar cututtuka. A yanzu haka tuni aka fara fama da cutar gudawa a tsakanin ‚yan gudun hijira ana kuma tsoron billar kwalera da zazzabin cizon sauro. Wani abin dake hana ruwa gudu wajen gabatar da taimakon shi ne tashe-tashen hankulan dake ci gaba da wanzuwa a kurkusa da yankunan da aka yi wa ‚yan gudun hijirar muhalli. Duk wanda yayi kurarin fita nemo kiraren wuta to kuwa zai shiga kaka-nika-yi game da makomar rayuwarsa, in ji Ulrike von Pilar. Matsalar tashe-tashen hankulan ba a Sudan ne kawai ta tsaya ba. A can kasar Afghanistan ma ainifin wannan matsalar ce ke hana ruwa gudu ga ayyukan taimako. Kungiyar likitocin ta kasa da kasa, tun a shekarar 1980 take gabatar da taimako ga kasar Afghanistan kafin ta dakatar da ayyukanta a kasar misalin makonni shida da suka wuce. Musabbabin haka kuwa shi ne kisan gillar da aka yi biyar daga cikin jami’anta a kasar a daidai ranar biyu ga watan yunin da ya wuce a daidai lokacin da suke kokarin gina wata tashar kiwon lafiya a lardin Badghis dake arewa-maso-yammacin Afghanistan. Wannan tsautsayi ya kada zuciyar illahirin ma’aikatan kungiyar ta taimakon magunguna kuma a sakamakon haka ta dakatar da ayyukanta a kasar Afghanistan nan take. Ba zata yarda ta sake kama ayyukan nata ba sai an samu kyautatuwar al’amuran tsaro a wannan kasa. Kazalika kungiyar ta ce maganar tsaro na daya daga cikin abubuwan dake ci mata tuwo a kwarya dangane da ayyukanta a yankin Kaukasiya, inda aka taba garkuwa da wani jami’inta har tsawon watanni ashirin kafin a sake shi a lokacin bukukuwan ista. Hatta a shekarar da ta wuce, kamar yadda rahoton na shekara-shekara ya nunar, reshen kungiyar a nan Jamus ya ci gaba da dogaro ne akan taimakon kudi daga daidaikun mutane masu zaman kansu domin gudanar da ayyukansa. Kungiyar tayi amfani da kudanden taimako na Euro miliyan 16 da ta tara domin gudanar da wasu shirye-shiryen taimakon da ta gabatar a kasashe 46, inda ta samu kafar kara yawan likitocin da take turawa domin aikin sa kai na gajeren lokaci a sassa dabam-dabam na duniya.