1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton shekara na kungiyar Kwadago ta dunia

Yahouza SadissouOctober 18, 2005

Haddadiyar kungiyar kwadago ta dunia ta bayyana rahoton ta na shekara da ta gabata.

https://p.dw.com/p/Bu4r

Kungiyar kwadago ta kasa da kasa, da ke da cibiyar ta, a birnin Brusells na Belgium, ta hiddo rahoton ta, na shekara- shekara, , a game da yadda membobin kungiyoyin kwadago na kasashe daban- daban a dunia su ka gudanar da ayukan su, a shekara da ta gabata.

A jimilce mutane, 145 ne, su ka rasa rayuka, a yayin da su ke cikin gudanar da yukan neman yancin ma´aikata, a yankunan su. 99 daga wannan mace- mace, sun wakana a kasar Kolombia.

Idan a ka kwatanta da shekara ta 2003, yawan mutane da su ka rasu, ya karu da mutum16.

Sannan a hannu daya, yawan membobin kungiyoyin da su ka samu barazanar kisa, shima ya hau, a cikin kasashe 137 da kungiyar ta gudanar da bincike.

Baki daya, kungiyar kwadago ta dunia, na da rassa a kasashe 152 da kuma kungiyoyin 233 membobin ta.

A banna ma, kamar bara kasashen da su ka fi kaurin suna, ta fannin taka hakokin ma´aikata sune, Zimbabwe da Tarayya Nigeria, Da Venezuella, da Hait,i da Kuma Jamhuriya Dominique, da Birmania, sannan akwai China, da Iran, da Belarussia a nahiyar turai.

Sakatare jannar na haddadiyar kungiyar kwadago ta dunia,Guy Ryder, ya ce gwagwarmayar neman kasuwa, daga kampanoni da masana´antu daban daban a dunia, ya hadasa tabarbarewar rayuwar ma´aikata, da karyar parashen aiki.

Sakataran ya nuna takaici matuka, a kan yadda a wasu kasashen shuwaghabanin ma´aikata ke fuskantar barazana iri iri, da a wani lokaci, ta kan kai su ga mahhalaka.

Ta wannan hanya ce, a Kambojia a ka hallaka shugaban kungiyar kwadago ta kasar, Chea Vichea.

A daya hanun kuma,ya ce kara kutsawar kasar China, a dandali kasuwa na dunia, na kara sa rudani da faduwar gaba a kungiyoyin ma´aikata.

Karancin albashi, da tsangwama, da kuma matsi da ma´aikatan kasar ta China, ke fuskanta, kan iya bazuwa ga sauran kasashen dunia ta wannan hanya.

Sakataran haddadiyar kungiyar kwadago, ta dunia ya bukaci shuwagabanin kampanoni, da da su kara mutunta hanyoyin tantanawa da kungiyoyin kwadago, domin itace hanyar da ta fi dacewa, ta cimma nasarorin warware matsalolin da kan tasowa tsakanin ma´aikata da masu kampanoni.

A nahiyar Afrika, inji rahoton, kashi 6 zuwa 25 ne bisa 100 kawai, na ma´aikata su ka tsara kansu, cikin kungiyoyi, duk da haka, gwamnatoci na yi masu kallon fittinanu, masu san tada zaune tsaye cikin kasa.

Rahoton ya kara da cewa, a kasashe Nigeria, Zimbabwe Botswana da Kenya, daruruwan ma´aikata sun rasa ayyukan su, a dalili da, sun gudanar da yajin aiki.

A wasu yankuna na gabas ta tsaykiya a cewar rahoton, kwata kwata ma, babu yanci kafa kungiyoyin ma´aikata, kamar a kasashe irin su Saudiyya , da Oman, sannan a Syria da Koweit doka ta bada izinin kafa kungiya daya ce tilo, ta kwadago abunda ke zaman koma baya, ga kwattata rayuwa ma´aikata.