Rahoton shekara na kungiyar ƙwadago ta ƙasa da ƙasa
June 6, 2006Mutane 115,yan gwagwarmayar ƙwatar yanci ma´aikata, su ka rasa rayuka, a shekara ta 2005, a sassa daban-daban na dunia.
Wannan alƙalumma, sun hito daga rahoton da haɗɗaɗiyar ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa da ƙasa, wato CISL, ta bayyana yau, a cibiyar ta, da ke birnin Brussels, na ƙasar Belgium.
Rahoton ya ce, bana,an samu ɗan ci gaba, idan a ka kwanta da shekara ta 2004, inda mutane 145 su ka mutu sanadiyar gwagwarmayar ƙwatar haƙƙoƙin ma´aikata.
Daga sahun ƙasashe 137 da a ka gudanar da bincike, a gano cewar, a ƙasar Colombia ne, ayyukan neman yancin ma´aikata ke tattare da haɗarruruka, fiye da ko inna cikin dunia.
A jimilce, yan ƙungiya 1.600 su ka fuskaci barzana kissa a shekara da ta wuce, a ƙasar, a yayin da aka tsaida 9.000.
Kazalika, ƙasashe kamar su Zimbabwe, Chine, Salvador Iran, Cambodjia, Djibouti da Gwatemala, na daga sahun wuraren da ƙungiyoyin ƙwatar yancin ma´aikata ke fuskantar uƙuba, daga gwamnati inji rahoton.
Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa da ƙasa, Guy Ryder, ya bayana matuƙar damuwa, a game da halin da mata ma´aikata, na ƙasar Colombia, ke gudanar da ayyukan yau da kullum cikin barazana.
Guy Ryder, ya suka da kakkausar halshe, ga magabatan ƙasashen Koweit, Oman, Qatar, saudi- Arabia, Lybia da Jordan, inda sam-sam ,babu damar girka ƙungiyoyin ƙwadago.