Rahoton Shekara Na Amnesty International | Siyasa | DW | 26.05.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rahoton Shekara Na Amnesty International

A yau laraba kungiyar kare hakkin dan-Adam ta Amnesty ta gabatar da rahotonta na shekara akan halin da ake ciki a game da makomar girmama hakkin dan-Adam a sassa dabam-dabam na duniya

Barbara Lochbihler Babbar Sakatariyar Reshen Amnesty Na Jamus

Barbara Lochbihler Babbar Sakatariyar Reshen Amnesty Na Jamus

A cikin rahoton nata na shekara kungiyar ta neman afuwa da kare hakkin dan-Adam Amnesty International a takaice tayi nuni da yadda makomar girmama hakkin dan-Adam ke dada fuskantar barazana a wannan duniya tamu. A fafutukar da suke yi na tsaron kan kasa, kasashe da dama kan wuce gona da iri tare da sa kafa su yi fatali da hakkin dan-Adam, kamar yadda aka ji daga bakin Barbara Lochbihler, sakatare-janar na reshen Kungiyar Amnesty a nan Jamus, a lokacin da take gabatar da rahoton kungiyar a birnin Berlin yau laraba. Ta ce azabtar da fursinoni da ake yi a Iraki da kuma yadda kasar Amurka ke tsagwamawa fursinonin da ta tsare a Afghanistan da Guantanamo, abu ne dake yin nuni a fili cewar hatta kasdashen dake ikirarin bin tsarin mulkin demokradiyya da girmama aikin doka ba sa shayin sanya kafa su yi fatali da yarjeniyoyi na kasa da kasa dake haramta azabtar da fursinoni. Jami’ar ta kara da yin kira kafa wata ‚yantacciyar hukuma ta kasa da kasa da zata yi bitar ta’asar azabtarwa da kisan fursinonin da aka fuskanta a kasar Iraki. A cikin rahoton kazalika Amnesty ta kalubalanci mahukuntan Jamus a game da azabtar da fursinoni sannan ta nema da a kafa wata cibiyar da zata rika bin diddigin lamarin domin hukunta duk wani mai sanye da rigar sarki da aka same shi da laifin cin mutuncin dan-Adam a kasar. Alkaluma na Kungiyar ta Amnesty sun nuna karuwar yawan kasashen da fursinoni kan sha fama da cin mutunci da azabtarwa a hannun mahukunta da misalin kashi daya bisa hudu, idan an kwatanta da bara waccan. A kasashe da dama akan tsare fursinoni ba gaira ba dalili. A shekarar da ta gabata an samu kasashe 44 da suka tsare fursinonin siyasa ba tare da wani dalili ba. A baya ga haka Amnesty ta gano wasu kasashe 47, a inda ko dai aka zartar da hukunce-hukunce na kisa ko kuma aka azabtar da fursinonin har lahira. Ko shakka babu kuwa a game da gaskiyar cewa adadin ya zarce hakan, saboda wannan kididdigar an gabatar da ita ne a hukumance. Dangane da ta’asar ta ‚yan tawaye kuwa, matsalar ta fi shafar mata, a kasashe 35 da Amnesty ta ba da bayani kansu. A wannan bangaren Amnesty ta ba da cikakken la’akari da halin da ake ciki a Kongo da yammacin kasar Sudan. Kungiyar tayi Allah waddai da kisan gillar da aka yi wa daruruwar farar fula da kuma fatattakar wasu dubban daruruwar daga yankunansu na asali a yammacin Sudan. Ta ce dakarun sa kai na Larabawa na samun rufa baya daga mayakan sama na gwamnatin Sudan, wadanda ke wa kauyuka a lardin Darfur ruwan bamabamai. Amnesty ta kara da sukan wasu kasashe na yammacin Turai, kamar Faransa, Birtaniya da Spain, wadanda ta ce tun bayan 11 ga watan satumban shekara ta 2001 suka gabatar da wasu dokokin yaki da ta’addanci da aka fita daga yayinsu suna masu kayyade ‚yancin jama’a a cikin gida. A lokaci guda kungiyar ta kare hakkin dan-Adam tayi Allah waddai da hare-haren kungiyar ta’adda ta Al-Ka’ida dake barazana ga makomar tsaro a duniya. Gaba daya dai kasashe 155 ne aka yi bayani dalla-dalla kansu a game da laifukansu na keta haddin dan-Adam.