1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton shekara na Amnesty International

May 18, 2005

Kungiyar Amnesty International, reshen Jamus, ta gabatar da rahotonta na shekara, inda take ci gaba da yin kira ga girmama hakkin dan-Adam tare kuma da kalubalantar gallaza wa fursinoni da aka yi karkashin matakan murkushe ta'addanci na kasa da kasa

https://p.dw.com/p/Bvbt
Irene Khan, babbar sakatariyar Amnesty a London
Irene Khan, babbar sakatariyar Amnesty a LondonHoto: AP

A cikin rahoton nata kungiyar Amnesty tayi kira da kakkausan hareshe ga mahukuntan Jamus da su dauki nagartattun matakai na kare makomar hakkin dan-Adam a kasar. Bai kamata kasar ta saduda ga matakan azabtar da fursinoni ko korar manema mafakar siyasa zuwa yankunan da ake fama da rikice-rikice a cikinsu da sauran manufofi na kabilanci da wariyar jinsi ba. A rahoton nata na bana kungiyar ta Amnesty ta mayar da hankali ne ga jama’a. Babbar sakatariyar kungiyar Babara Lochbihler tayi nuni da yadda ake ci gaba da tsaurara matakan gallaza wa mutane a karkashin manufofin nan na murkushe ta’addanci. Ta ce wajibi ne mutane su tashi tsaye domin mayar da martani akan wadannan matakai, inda mahukunta ke fakewa da guzuma domin su harbi karsana. Ita dai kungiyar Amnesty, har kwanan gobe, ba zata yi watsi da shikashikan ayyukanta na adawa da matakan azabtar da fursinoni da hukunce-hukunce na kisa da kuma kame-kame na ba gaira ba dalili ba. A halin yanzu haka maganar Sudan, musamman lardinta na Darfur, ita ce ta fi ci wa kungiyar Amnesty tuwo a kwarya. Alkaluma masu nasata da MDD sun ce kawo yanzu mutane kusan dubu 30 suka yi asarar rayukansu, sa’annan wasu miliyan biyu suka yi hijira, sakamakon rikicin da yaki ci ya ki cinyewa a lardin na Darfur. A lokacin da yake bayani a game da halin da ake ciki a Darfur Alfred Buss, kwararren masanin kungiyar Amnesty akan al’amuran Sudan karawa yayi da cewar:

2. O-Ton Buss

“Die Menschenrechtssituation…

Ana cikin mawuyacin hali a game da hakkin dan-Adam. Babban dalili kuwa shi ne kasancewar yau tsawon shekaru da dama ke nan kasar Sudan na karkashin dokar ko-ta-kwana ta soja, a yayinda a can yammacin kasar kuma aka kafa dokar ta bace.Hakan na ma’ana ne cewar jami’an tsaro na da ikon cafke fursinoni, kama daga ‘yan hamayya zuwa ga ‘yan arida sakamakon ra’ayinsu da ya banbanta da na gwamnati akan wata manufa ta siyasa.

Wannan maganar, kamar yadda kungiyar Amnesty ta nunar, ta hada har da yankunan arewaci da gabacin Sudan, inda gwamnati ke tace rahotanni da kayyade ayyukan kafofin yada labari da gallazawa fursinoni hade da azabtarwa da kuma kisan ba gaira akan masu zanga-zanga da akan tsare a gidajen wakafi. Kungiyar kazalika ta dade tana mai fafutukar ganin an kyautata makomar jin dadin rayuwar jama’a a kasar Irak, mai fama da tabarbarewar al’amuranta na tsaro. Wani abin da Amnesty tayi orafi game da shi kuma shi ne kashe-kashe na gilla da aka yi wa mata a kasar ta Irak, wai sabota sun keta hurumin danginsu. A wannan bangaren kungiyar tayi kira ga kafofi na kasa da kasa da su yi bakin kokarinsu wajen dakatar da wannan cin mutuncin da ake wa mata a kasar ta Irak.