Rahoton shekara na Amnesty International | Siyasa | DW | 23.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rahoton shekara na Amnesty International

A cikin rahotonta na shekara kungiyar Amnesty tayi kira da a bi manufofin demokradiyya mai dorewa

Duk dai wanda yayi zaton cewar duniya zata samu zaman lafiya da kwanciyar hankali bayan kawo karshen zaman dardar tsakanin kasashen yammaci da na gabacin Turai, tuni murnarsa ta koma ciki. Domin kuwa abubuwa masu tarin yawa sun ci gaba da faruwa suna kuma barazana ga makomar zaman lafiya da walwala a duk fadin duniya. A yau ma dai duniyar ta kaso ne zuwa rukunoni guda biyu, rukunin matalauta ‘yan rabbana ka wadatamu da kuma rukunin mawadata masu hannu da shuni. Hakan shi ne ya haifar da wani sabon yanayi na zaman dardar da juna, inda aka wayi gari mawadatan ke fargabar gushewar abin da suka tara sakamakon guje-gujen hijira da tuttudowar baki da ta’addanci da makamantansu. A cikin rahotonta na bana kuma a karon farko kungiyar neman afuwa ta Amnesty International ta fito fili tayi batu a game da yadda take hakkin dan-Adam a fannoni na tattalin arziki da zamantakewa ke rura wutar rikice-rikice da yake-yake da kuma yadda jami’an siyasa ke tsorata mutane suna masu jefa su cikin rudami da rashin sanin tabbas a sassa daban-daban na duniya. Fargaba kamar yadda aka sani ta kan jefa mutum cikin rudami wanda kuma shi ne ainifin ummal’aba’isin wariya da kabilanci da nuna banbancin launin fata da farautar tsiraru. A cikin rahoton nata dai Amnesty ta ba da misalai da dama a dukkan nahiyoyin duniya. Misali an dade Amurka na bakin kokarinta wajen danne gaskiya akan abin dake faruwa a sansanin gwale-gwalenta na Guantanamo, a yayinda a yankin gabas ta tsakiya aka sake shiga wani sabon yayi na danne ‘yancin fadin albarkacin baki. A can Rasha kuwa ‘yan jarida da masu fafutukar kare kewayen dan-Adam suka shiga kaka-nika-yi a game da makomar rayuwarsu. Su kuwa shuagabannin Iran tsoro suke a game da ‘yancin mata a kasar. Wannan maganar ma ta shafi har da kasashen Afghanistan da Pakistan da kuma Sudan, inda masu fafutukar kare hakkin mata kan shiga hali na kaka-nika yi a duk lokacin da suka yi kurarin nuna adawa da wasu matakai na danniya da keta haddin mata. Kazalika a sakamakon faragabar hare-haren ta’addanci ake wuce gona da iri a matakan tsaron da ake dauka dangane da taron kasashen G8 da za a gudanar a nan Jamus, yadda lamarin ya kai ga fatali da wasu dokoki na kare hakkin jama’a. A sakamakon haka Amnesty ke gabatar da kira a game da mayar da hankali akan wasu manufofin da zasu taimaka wajen dorewar demokradiyya da kare hakkin dan-Adam, kuma wannan shi ne abin da ya kamata shuagabannin gannan kasashemn guda takwas ya kamata su dukufa akai a taron kolin nasu a Heiligendamm wata mai zuwa.