1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Rahoton shekara na ƙungiyar UNESCO

A rahoton da ta fitar ƙungiyar bunƙasa Ilmi, kimiyya da a'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO ta ce yara kimanin miliyan 67 ne a duniya baki ɗaya har yanzu basu sami damar shiga makaranta ba

default

Yara manyan gobe

Rahotan na UNESCO yace daga cikin wannan adadi na yara miliyan 67 da basu sami shiga makaranta ba, yara miliyan 28 suna zaune ne a ƙasashe waɗanda ke fama da tashe tashen hankula.

Ilmi haƙƙi ne da ya kamata kowane ɗan Adam ya kasance ya samu. Kamar sauran alƙawuran gamaiyar ƙasa da ƙasa cewa Ilmi abu ne da kowane mahaluki ya kamata ya samu, har yanzu ba'a kai ga cimma wannan buri ba. A babban taron duniya da aka gudanar a Dakar a shekara ta 2000, ƙasashe 164 sun rattaba hannu akan ƙudirin samar da ilmi ga jama'arsu zuwa shekara ta 2015. Farfesa Christoph Wulf na Jami'ar Majalisar Ɗinkin Duniya a Berlin kuma shugaban kwamitin Ilmi na hukumar UNESCO a nan Jamus ya yi tsokaci da cewa:

Schule in Afrika

Yara 'yan makaranta a Nairobi

" Ba za'a iya cimma wannan ƙudiri ba, ko da yake an yi matuƙar ƙoƙari kuma an cimma wasu nasarori. Akwai matakai guda shida waɗanda ya kamata dukkaninsu a samar da su domin kaiwa ga nasarar samar da Ilmin ga jama'a. Waɗannan kuwa sun haɗa da sanya ruhin ilmin ga yara tun suna ƙanana da samar da ilmin ga kowa a matakin farko da kare buƙatun Ilmin ma'ana samar da abinci mai cike da ƙoshin lafiya ga yara domin sai sun ƙoshi ne za su sami sukunin mayar da hankali ga koyon karatun da samar da daidaito a tsakanin jinsin Maza da Mata sannan da inganta martabar Ilmin ya zamo mai nagarta".

Babban abin damuwa a cewar Farfesa Wulff shine cewa ana samun naƙasu a ƙasashe waɗanda walau dai suna cikin yaƙin basasa ko kuma basu gama farfaɗowa daga yaƙin basasar ba.

" Kana iya amfani da ilmin domin faɗakar da al'uma ko kuma akasin haka. misali za'a sami cimma burin dimokraɗiyya ne kawai idan jama'a suka sami ilmi ingantacce, ta yadda za su fahimci abinda ke faruwa a kusa da su, su kuma iya bainya 'yancinsu a siyasance. Idan ba'a yi haka ba, to a iya cewa ma babu dimokraɗiyyar".

Ƙungiyoyin agaji da dama sun soki rahoton na bana na UNESCO dake cewa za'a samar da ƙarin taimakon jin ƙai ga wasu muhimman sassa kuma mutane da dama a waɗannan yankuna za su amfana. Bugu da ƙari suka ce akwai ayar tambaya wajen gwamutsa harkar rundunar tsaron ƙasa da ƙasa da kuma harkar Ilmi. Alal misali ƙungiyoyin suka ce makarantun da suke ƙarƙashin kulawar sojojin ketare sun fi fuskantar barazanar hare hare akan makarantun dake ƙarƙashin kulawar jami'an tsaro na wannan ƙasa kamar yadda Mike Lewis na ƙungiyar agaji ta Oxfam ya nunar:

Didacta 2011 Februar

" Babbar matsalar ita ce ba wai ga ayyukan mu ko kuma jami'an mu ba, a'a amma tsare lafiyar jama'ar dake wuraren da muke aiki. Ba kawai a Afghanistan ba kaɗai harma sauran wurare da ake fuskantar tashe tashen hankula a sassan duniya, muna ganin irin wannan ruɗani tsakanin muradun sojin da kuma buƙatu na jin ƙan al'uma mazauna wurin.

Hukumar ta UNESCO ta koka a sabon rahoton game da ƙaruwar fashi a makarantu. A ƙasashe kamar Afghanistan da Pakistan yara mata kan rasa rayukansu a hare haren da ake kaiwa makarantun. A wasu lokutan kuma akan yiwa iyayensu baraza matuƙar basu janye su daga makaranta ba. A dai ƙasashe da ake yakin basasa ana yawan kai farmaki makarantu, a sace yara, maza a sanya su aikin soji na dole yara mata kuma a yi musu fyaɗe a kuma sanya su aikin bauta a gidaje, saboda haka idan ba'a sami Ilmi da wayewa ba haka za'a riƙa samun koma baya a irin waɗannan al'umomi.

Idan dai babu Ilmi to tamkar babu makoma kyakyawa. Yawaitar tarzoma kuma ka iya kaiwa ga yaƙin basasa. Haka dai za'a yi ta samun kwan gaba kwan baya a saboda haka Ilmi ba ma kawai ya kasance tafarkin samun zaman lafiya bane kaɗai harma da wanzar da cigaba mai ma'ana a ƙasa.

Mawallafa: Helle Jeppesen/Abdullahi Tanko Bala
Edita Mohammad Nasiru Awal