Rahoton shekara na ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama ta duniya | Siyasa | DW | 27.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rahoton shekara na ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama ta duniya

Har yanzu take haƙƙin bil Adama na cigaba da zama ruwan dare a wasu ƙasashen duniya.

default

Monika Lüke Sakatariyar ƙungiyar Amnesty rashen Jamus

Shekara ta 2009  akwai faranta rai, a wani ɓanggaren kuma har yanzu yan siyasa na ci gaba da kawo koma baya bisa abinda ya shafi kare haƙƙin bil'adama, kuma dolene a yi yunƙuri kawo ƙarshen muzgunawa jama'a wannan shine abinda ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty ta gabatar a rohotonta bayan alƙaluiman da ta tattara na shekarar.

Shekarar bara ta fara ne da sammacin kamo shugaban ƙasar Sudan wanda kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta bayar, wanda shine karo na farko da kotun ta nemi a gabatar mata wani shugaba dake kan mulki, amma hakan ya samu Allah wadai daga ƙasashen Afirka waɗan suka marawa Albashir baya.

Sakatariyar ƙungiyar Amnesty rashen ƙasar Jamus Monika Lüke ta bayyana cewa, daga cikin ƙasashen da suka sanya hannu bisa kare haƙƙin bil'adama a duniya, har aka kafa kotun hukunta masu aikata manyan laifuka wato ICC, za'a iya cewa har yanzu batun kare haƙƙin bil'adama yana buƙatar gyara. A faɗar ta ƙasashen sun haɗa da Amirka da Rasha da China da Indonisiya da Turkiya, inda tace lallai ne a samu sauyi daga waɗannan ƙasashe wajen cin zarafin bil'adama.

"Saƙon da ke kumshe a kotun hukunta masu aikata manyan laifuka, shine batun cin zarfin bil'adama, ga waɗanda yan siyasa suke muzgunawa da turasu gidan yari. Dole a kawo ƙarshen wannan matsalar, babu wanda yafi ƙarfin a hukunta shi, kuma dole a baiwa waɗanda aka cutar yancinsu."

Lüke ta kuma bayyana ƙasashen Sirilanka da Isra'ila da yankin Falasɗinawa da Jamhuriyar Dimokraɗiyar Kwango da Rasha a mtsayin ƙasashen da suke kan gaba wajen ƙeta haƙƙin bil'adama

"Idan mutum ya dubi abinda ke faruwa Mosko da yankin Kaukasous, to babu irin ƙeta haƙƙin bil'adama da ba ayi harma da kisa"

ein Jahr Obama Flash-Galerie

Masu zanga zanga dake bukatar a rufe sansanin gwale-gwale na Gwantanamo dake Cuba

Rohoton ya kuma soki ƙasar Amirka musamman rashin cika alƙawarin da shugaba Obama yayi na rufe sansanin Guantanamo inda ake tsare da fursunoni ba tare da yanke musu shari'a ba.

Kimaniun fursunoni 50 ke tsare a Guantanamo har yanzu, kuma ba'a gabatar da su a kotu ba, kana wai za'a kaisu jahar Ilinois, to mi akayi kenan ai ba saiyi, kana waɗanda suka bada umarni aci zarafin fursunonin a zamanin gwamnatin Bush har yanzu sunanan ba'a hukuntasu ba"

Sakatariyar ƙungiyar Amnesty rashen Jamus ta kuma bayyana ƙasar Iran, da cewa shekara ta 2009 wata mummanar shekara ce ga yancin bil'adama

"Hasalima bayan zaɓen ƙasar na 12 ga watan juni, musgunawa al'ummar Iran da yawa, kuma har yanzu Ahmadinajad yana ci gaba da riƙe ikon shugabancin ƙasar, kimanin yan adawa 300 suna ɗaure a gidan yari ba tare da an yanke musu hukunci ba, mata suna ta fiskata fyaɗe"

A bisa yunƙurin sasantawa tsakanin Karzai da yan Taliban na ƙasar Afganistan Amnesty tace batun kare haƙƙin bil'adama shi yakamata a sanya gaba, don an fara samun ci gaba.

"Amnesty tana gudun yancin mutane yana fiskantar ci gaba , musamman ta fannin mata, domin ada ba'a samun abinda ake ganin yanzu zaman Talöiban"

Sai dai rohoton ya bayyana samun cigaba ta bangaren kare haƙƙin bil'adama a ƙasashe kamar Sudan da Jamus duk da cewa dai da sauran batutuwan da har yanzu suke buƙatar samun gyara.

Mawallafa : Sabine Ripperger / Usman Shehu Usman

Edita : Umaru Aliyu