Rahoton MDD Akan Cutar Aids | Siyasa | DW | 06.07.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rahoton MDD Akan Cutar Aids

Cutar Aids mai karya garkuwar jikin dan-Adam sai dada tsamari take yi a yayinda jami'an siyasa kuma suka kasa daukar nagartattun matakai domin tinkarar matsalar

Alkaluma da aka tara sun nuna cewar kusan a baya ko wace dakika goma sai an samu wani mutumin da zai jirkata daga cutar ta Aids ko kuma mai kamuwa da kwayoyinta bayan dakika shida. Kuma ko da yake har yau masana na ci gaba da lalube a cikin dufu a kokarin nemo maganin cutar ba tare da nasara ba, amma fa akwai hanyoyin da suka dace domin riga kafinta kamar dai wayar da kan jama’a game da ita. Muhimmin abin da ake bukata shi ne isasshen kudi domin aiwatar da wadannan matakai. Kazalika akwai bukatar ba wa mutane cikakken ikon shiga ana damawa da su a duk wani matakin da za a dauka domin dakatar da yaduwar wannan ummal'aba'isi da ta zamewa duniyar kayar kifi a wuya, sai kuma hadin kai tsakanin masana’antun sarrafa magunguna. Dukkan wadannan gibi wajibi ne a cikesu kafin kwalliya ta mayar da kudin sabulu. Wasu rahotanni da aka samu sun yi korafin cewar ko sau daya ba a taba jin kalmar Aids ta fito daga bakin shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ba duk kuwa da yaduwar da cutar ke ci gaba da yi tsakanin al’umar kasar ba kakkautawa. A sakamakon yaduwar cutar a kasar Rasha da kasashen nahiyar Asiya, daga baya-bayan nan, bankin duniya tayi kira a game da daina sako-sako da wannan matsala a kasashen da lamarin ya shafa. Misali kawo yanzu babu wata gwamnati a kasashen Indiya ko Afghanistan ko Nepal ko Sri Lanka da ta gabatar da wani takamaiman shiri domin tinkarar cutar ta Aids duk kuwa da cewar tuni cutar ta fara rutsawa da wadannan yankuna. Su ma kasashen yammaci har yau suna daridari da lamarin. Sun ki su cika alkawarin da suka yi na gabatar da kudade ga asusun da MDD ta kirkiro domin amfani da su wajen yaki da cutar a duk fadin duniya. Wannan halayya ta ko oho ita ce ta kai yankin kudancin Afurka ta baro. Kauyuka da unguwanni duk sun watse saboda cutar tayi awon gaba da mazauna cikinsu. Zaka tarar da matasa a cikin hali na kaico sakamakon kamuwa da kwayar cutar tun kafin su kammala makarantu na sakandare ko kuma kakanni na kula da renon cikokinsu, wadanda suka rasa iyayensu daga cutar ta Aids. A halin yanzu haka tuni wannan annoba ta canza tsarin zamantakewar jama’a tare da raunana matsayin tattalin arziki da gaggauwa yaduwar matsalar talauci a kasashen yankin na kudancin Afurka. Amma fa kamar yadda muka yi bayani tun farko, cutar ba kawai nahiyar Afurka ce take addaba ba tuni ta zama ruwan dare a wannan duniya tamu. Abu mafi alheri domin dakatar da wannan mummunan ci gaba shi ne biyayya ga tsare-tsaren da kungiyar kiwon lafiya ta MDD da hukumar Majalisar akan cutar Aids suka gabatar. Amma a bin takaici shi ne yadda kasashen yammaci ke fatali da lamarin. Misali shugaba Goerge W. Bush na kasar Amurka yana adawa da shirye-shiryen na MDD saboda ya dadada wa ‚yan mazan-jiya dake ba wa jam’iyyarsa goyan baya lokacin zabe. Shi kuma shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder ya kan yi nuni da matsalar karancin kudi a baitul-malin gwamnatinsa wajen kin biyan gudummawar da kasar tayi wa MDD domin yaki da cutar ta Aids. Ita kuwa China har yau tana kuwa China har yau tana ci gaba ne da rufa-rufa a game da yaduwar wannan cuta a kasar.