Rahoton Majalisar dinkin duniya akan cutar AIDS | Labarai | DW | 21.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rahoton Majalisar dinkin duniya akan cutar AIDS

Wani rahoton MDD yace kimanin wasu mutane miliyan 4 .3 suka kamu da kwayar cutar HIV cikin 2006 a duniya baki daya,wanda ya kawo yawan wadanda suke da cutar a duniya kusan mutum miliyan 40.

Rahoton yace an samu karuwar yawan mata da suka kamu da cutar.

Yankunan da aka fi samun karuwar cutar sun hada da kasashen tsohuwar taraiyar Soviet,da kudanci da kuma kudu maso gabashin Asiya,yawancinsu sakamakon tuammali da miyagun kwayoyi da kin yin anfani da kwaroron roba.

Kasashern Afrika daker kusa da sahara har yanzu suna fama da balain annaobar cutar ta AIDS inda yanzu haka mutane akalla miliyan 25 suke dauke da cutar,wanda yake kusan kashi 2 bisa 3 na wadanda suke da cutar a duniya baki daya.

Rahoton yace an samu ingancin hanyoyin samarda magungunan cutar cikin yan shekarun baya bayan nan.