1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton Majalisar Dattawan Amurka Akan Tabargazar Da Hukumar CIA Ta Caba

July 12, 2004

Da kakkausan harshe majalisar dattawan Amurka ta soki lamirin hukumar leken asiri ta CIA dangane da rahotonni na kage da ta bayar domin share hanyar kai farmaki kan kasar Iraki ba gaira ba dalili

https://p.dw.com/p/BviE

In dai ba a manta ba a misalin shekaru biyu da suka wuce, lokacin da rikicin kasar Iraki ya fara fuskantar intaha, masu kaunar tinkarar kasar da yaki suka rika aron bakin hukumar CIA domin ginshikin manufarsu. Kamar dai yadda suka nunar, wai hukumar ta leken asirin kasar Amurka ta tara cikakkun rahotanni da bayanan dake tabbatar da cewar tsofon shugaban kasar Iraki Saddam Hussein ya dirke muggan makamai na guba kuma yana kan hanyar sarrafa makaman nukiliya. Dakatar da wannan shiri nasa shi ne kawai zai taimaka wajen hana wanzuwar wani bala’i a wannan yanki da Amurka da ma duniya baki daya. A wancan lokaci dai masu adawa da manufar yakin ba su yi wata-wata ba wajen karyata wannan rade-radi da shaidar da ake yayatawa. Amma fa yau sai ga shi an wayi gari majalisar tattawan Amurka na mai tabbatar da wannan karyar da aka rika yayatawa. Rahoton dake dauke da tambarin majalisar dattawan ta Amurka yayi nuni da cewar hukumar leken asirin ta CIA ba ma kawai wuce gona da iri tayi ba, kazalika ta nuna son kai da jirkita gaskiyar halin da ake ciki da kuma dogaro akan wasu majiyoyin da ba su da tushe. Hukumar ta gabatar da rahotanni na kage, wadanda suka share wa shugaba Bush hanyar gabatar da matakinsa na yaki da halaka dubban daruruwan mutanen da ba su san hawa ba ba su kuma san sauka ba tare da jefa kasar Iraki cikin hali na rudu da rashin sanin tabbas. Hukumar leken asirin ta Amurka ita ce ta ba da lasin din wadannan kashe-kashe na gilla. A nata bangaren gwamnatin shugaba Bush ba zata yi wata-wata ba wajen amfani da wannan rahoto domin wanke kanta daga alhakin yakin, inda zata yi ikirarin cewar ta wanzar da abun da hukumar leken asirin ta gabatar mata ne kawai, ba ragi ba kari. Amma fa abin lura a nan shi ne, ko da yake majalisar dattawan ba ta da shaidar dake tabbatar da tasirin gwamnatin Bush akan ayyukan hukumar ta leken asiri ta CIA, amma fa dukkan hukumomin leken asirin kasa, kafofi ne na gwamnati dake taka rawa a matakan da take dauka bisa manufa. Ita hukumar ta CIA ta wanzar da alhakin da shugaba Bush da mataimakinsa Cheney da sakataren tsaro Rumsfeld suka dora mata ne na nemo wata shaidar da zata ba su kafar kai farmaki kan kasar Iraki da jan kunnen tsofon shugabanta Saddam Hussein. Ganin haka ya zama tilas akan hukumar ta CIA ta ba da shaidar zul, tun da yake kasar ta Iraki a hakika ba ta mallakar makaman kare dangi. Amma ba hukumar CIA ce kadai ke da laifi ba hatta su kansu kafofin yada labarai da ‚yan hamayya na Democrats sun gaza saboda sun kasa bin diddigin rahotannin hukumar domin nemo gaskiyar lamarin da hana wanzuwar wannan tabargaza, wacce tayi sanadiyyar rayukan dubban daruruwan mutane ba gaira ba dalili ta zubar da martabar Amurka a idanun duniya da kuma mummunar kiyayyar kasar a kasashen Musulmi.