Rahoton Kwamitin Kula Da Al′amuran Kaka-Gida A Jamus | Siyasa | DW | 08.07.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rahoton Kwamitin Kula Da Al'amuran Kaka-Gida A Jamus

Kwamitin kula da manufofin kaka-gida a Jamus yayi marhabin da sabuwar dokar kaka-gida da aka gabatar baya-bayan nan, wacce suke fata zata taimaka wajen kyautata cude-ni-in-cude-ka tsakanin Jamusawa da takwarorinsu baki

An saurara daga bakin farfesa Klaus Bade daga cibiyar nazarin manufofin kaka-gida a garin Osnabrück dake nan Jamus, wanda kuma ke daya daga cikin wakilan kwamitin kwararrun da gwamnati ta nada, yana mai Hamdallah a game da cewar Jamus dai ta wayi gari tana da wata takamaimiyar doka dake daidaita ka’idojin kaka-gida a kasar. A baya ga kasancewar dokar tana mai amincewa da kaka-gida, kazalika zata taimaka wajen kyautata cude-ni-in-cude-ka tsakanin Jamusawan da bakin da suka dade suna masu kaka-gida a kasar ta Jamus. Farfesa Bade ya ce wannan babban ci gaba ne da wajibi ne a yi madalla da shi idan aka yi la’akari da yadda aka sha famar kai ruwa rana akan wannan batu. To sai dai kuma Bade da takwarorinsa a kwamitin rikon kwarya sun yi nuni da babban gibin dake akwai a tsarin dokar. Domin kuwa a yanzu an shiga wani sabon yanayi ne na wawason kwararrun masana a duk fadin duniya, kuma sauran kasashe masu ci gaban masana’antu sun gabatar da nagartattun dokokin dake ba wa wadannan kwararrun masana damar kaka-gida a cikinsu ba tare da ka ce na ce ba. Amma ita dokar ta Jamus ba ta goge kudurin dakatar da dauko ma’aikata daga ketare ba, a maimakon haka sai aka ci gaba da kame-kame da zayyana wasu sharudda game da wannan batu. Abin marhabin game da sabuwar dokar, kamar yadda aka ji daga bakin Marieluise Beck, wakiliyar gwamnati akan al’amuran kaka-gida, shi ne damar da take ba wa dalibai baki na ci gaba da zamansu a Jamus bayan sun kammala karatu a jami’o’in kasar. Kazalika dokar ta kunshi garambawul domin kyautata makomar ‚yan gudun hijirar dake neman mafaka a Jamus. A karkashin dokar Jamus zata rika karbar bakuncin ‚yan gudun hijirar dake kauracewa daga kasashensu bisa dalilai na muzantawar ‚yan tawaye ko wasu dalilai dabam da ba su da nasaba da manufofin gwamnatin kasashen nasu. Wani abin da kwararrun masanan su 30 suka kuma yi marhabin da shi shi ne matakan da dokar ta tanadar game da kara kyautata manufofin cude-ni-in-cude-ka tsakanin ‚yan kaka-gida da takwarorinsu Jamusawa. Amma kuma sun yi gargadi a game da neman wuce gona da iri wajen shirya ire-iren kwasa-kwasan nan na koyan harshe. Bisa ga ra’ayin kwararrun kwasa-kwasai na yaki da jahilci a game da harshen Jamusancin zai wadatar. Abu mafi alheri shi ne a samu sauyi a zukatan Jamusawa a ma’amallarsu da baki ‚yan kaka-gida a kasar, saboda hakan na daya daga cikin abubuwan dake hana ruwa gudu wajen samun kyakkyawar kusantar juna tsakanin sassan biyu.