Rahoton kungiyar gamayar turai a game da baki yan cirani
October 19, 2005Talla
Hukumar kungiyar gamayyar turai ta bayyana wani rahoto a game da baki yan ci rani, na assulin kasashen da ke kewaye da kogin Mediterane, wanda a halin yanzu ke zaune a kasashen turai, bisa ka´ida.
Rahoton yace a jimilce, baki million 5 zuwa million 6 darabi ne, daga wannan kasashe, ke zaune a nahiyar turai.
Kashi 3 bisa 4, na wannan mutane na aiki a nan Jamus da Fransa.
Daga cikin kasashe 10 da rahoton ya shafa, Turkawa sun fi yawa a nan turai, sannan, sai yan kasar Marroko da yan Algeria.
Rahoton ya ce mafiyawan wannan baki, yan ci rani, na ayyuka a wuraren da su ka shafi lebranci, da aikin gona, da yan share share, da dai sauran ayyukan da turawan basu bukatar yi.