Rahoton komitin majalisar turai ya zargi kasashen turai 11 da hannu cikin aiyukan CIA | Labarai | DW | 28.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rahoton komitin majalisar turai ya zargi kasashen turai 11 da hannu cikin aiyukan CIA

Wani rahoton komitin musamman na majalisar taraiyar turai ya jera sunayen kasashen turai 11 wadanda suke da masaniya game da sace wadanda ake zargi da taaddanci da hukumar CIA takeyi tare kuma da mallakar gidajen fursunan na sirri a turai.

Kakakin komitin Claudio Fava yace kasar Jamus da Burtaniya da Italiya suna cikin kasashen da suke da hannu dumu dumu ko kuma a fakaice cikin wannan alamari amma sunyi gum da bakinsu.

Fava ya kara da cewa a 2005, sakatariyar harkokin wajen Amurka Condileeza Rice ta sanarda kasasahen KTT wajen wani taron KTT da NATO game da wannan batu.

Rahoton wanda ya fito bayan watanni 6 na bincike ya kuma yi suka ga wasu manyan jamain KTT kamar Javier Solana saboda boye irin wadannan bayanai.