1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rahoton komitin kare aikin jarida ta kasa da kasa

Kungiyar kare aiyukan yan jarida ta kasa da kasa,ta fito da rahotansa na shekara ,tana mai zargin gwamnatocin kasashe da laifin nuna iko da tsokana tare da yiwa kafofin yada labaru takunkumi a aiyukansu.

default

Kama daga batun kara karfin iko kan aikin jarida a Rasha da kafa dokokin rage anfani da yanar gizo a kasar China,kungiyar mai hedkwata a birnin New York,tace gwamnatoci suna ci gaba da canzawa daga hani a fakaice zuwa wasu hanyoyi na daban wajen kafa takunkumi akan wadanda suke suka ga manufofinsu.

Rahoton yace duk da cewa dokar kasa da kasa ta bada kariya ga yan jarida,wannan doka baa aiwatar da ita,a zahiri ma zaa iya cewa a rubuce ne kadai take aiki.

Babban darektan kungiyar Joel Simon yace ababenda suke faruwa a Iraki da Lebanon sun kara baiyana yadda yan jarida suka kau daga matsayinsu nay an baruwanmu,inda yace a rikicin Iraki,mafi muni gay an jarida,sau da yawa sojin sa kai sun kashe yan jarida da saninsu ba bisa kuskure ba.

Hakazalika dakarun Amurka a Irakin sun kashe yan jarida 14 da gangan,kuma babu wani bincike da rundunar sojin ta Amurka ta kaddamar game da wannan zargi.

Darektan yace,yan jarida maimakon dogara da dokar kasa da kasa da hana kashe yan jarida wajen yaki,sun dogara ne kan alkawura da suke baiwa bangarori dake yaki da juna na cewar zasu baiyanawa duniya sakoninsu.

Rahoton ya baiyana shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez da Vladmir Putin na Rasha a matsayin manyan masu laifi kan wannan batu,wadanda a cewar rahoton suke shugabanin da suka fi kawo cikas tare da kafa takunkumi akan kafofin yada labaru.

Kungiyar tace a kasar Rasha an kashe yan jarida 13 tun lokacinda Vladmir Putin ya karbi shugabancin kasar a 2000,kuma babu wanda aka kama da wannan laifi,abinda ya sanya yan jarida a akasar suke dari darin yin bincike game da wasu rahotanni ko kuma ma yin watsi da wasu labari masu muhimmanci,yayinda Putin yake cin moriyar wannan tsoro da suke nunawa.

Rahoton yace wasu kasashen sun daure yan jarida da suke suka ga manufofinsu,yana mai bada misali da kasar Iran wadda ta rufe gidan jaridu fiye da 100 tare da rufe yan jarida da dama a kurkuku tun 2000.

Duk da cewa ta sake su bayan dan kankanin lokaci,amma har yanzu da sauran rina kaba game da yiwuwar sake tsare su.

Rahoton ya kara da cewa,akwai kuma kasashe da har yanzu suke anfani da karfin tuwo,wajen musgunawa yan jarida,kasashe kamar Cuba da Eritrea,suna daga cikin irin wadannan kasashe inda yan jarida da dama suke shiga masifu iri dabam dabam.

Yayinda kasar china kuma inji rahoton take daukar tsauraran matakai na kare wasu muhimman labari kaiwa ga jamaarta.

Rahoton ya zargi gwamnatoci da nuna halin ko in kula game da kashe yan jarida da dama,yana mai baiyana cewa babu wani da aka kama da laifi na kashi 85 cikin dari na yan jarida da da aka kashe.

 • Kwanan wata 05.02.2007
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtwO
 • Kwanan wata 05.02.2007
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtwO