1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton karshe kan illolin dumamar yanayi

April 6, 2007
https://p.dw.com/p/BuO7

Manyan masana ilmin kimiya na duniya sun kammala shirya rahotonsu kann illar dumamar yanayi a duniya.

Komitin kasa da kasa na kwarraru kann yanayi sunce dumamar yanayi zai shafi rayukan jamaa da dabbobi cikin wannan karni.

Yace illar da hayakin masanaatntu zai yiwa yanayi zai canza tsarin ruwan zai kuma haddasa ruwan sama da iska mai karfin gaske,tare da kara barazanar fari da ambaliyar ruwa.

Rahoton yace kusan kashi 30 cikin dari na dabbobi da tsirrai zasu shafe daga doron kasa.

Masana kimiyya fiye da 2,500 wadanda suka shirya wannan rahoto sun kuma hasashen cewa biliyoyin mutane zasu fuskanci karancin ruwan sha miliyoyi kuma zasu kara shiga matsalar yunwa.

Masu binciken sunce canjin yanayi dana muhalli zai fi shafar matalauta.