1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton ICG a game da Nigeria

October 26, 2006
https://p.dw.com/p/BueU

Hukumar ƙasa da ƙasa ta International Crisis Group, ta wallafa wani rahoto a game da Taraya Nigeria.

Rahoton ya nunar da cewa tsarin mulkin ƙasar, da aƙidar Federaliya, da ta ke bi, na matsayin barazana, ga ɓarkewar riginginmu, da kuma darewar ƙasar.

Mudun hukumomnin wannan ƙasa, mafi yawan jama´a da man petur a Nahiyar Afrika, basu ɓullo da wassu sabin hanyoyi ba, na gudanar da harakokin mulki, da kuma yaƙi ,da cin hanci da karɓar rashawa, hukumar ICG, ta ce ta rumtse ido, ba ta ga ken makamta ba , ga makomar Nigeria.

Rahoton hukumar ICG, ya zargi gwamnatin tarayya, da shinfiɗa mulki bisa dogaro da aƙidojin addini, da na ƙabila, sannan magabatan ƙasar, na ci mattuƙa gayya, da gumin talakawa.

Jimmilar wannan al´amura sun hadasa sakamako mummuna, tare da aifar da ƙungiyoyin zawaye barkatai a yankuannda dama na kasar.

A ƙarshe, rahoton ya ce idan gwamnati bata tashi tsaye ba, tsayin daka, ta lallubo hanyoyin daidaita sahun harakokin mulki a Nigeria,ƙasar zata shiga wani halin ni ya su, mussamman, ta la´akari da shirye shiryen zaɓen, da a ke sa ran gudanarwa, a shekara mai zuwa.