1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton hukumar samar da makamashin Nukliya ta duniya akan Iran

November 9, 2011

Iran ta ce ba za ta dakatar da shirin ta ba na Nukliya duk da rahoton da hukumar ta IAEA ta ke shirin baiyana wa a hukumce wanda ke zargin ƙasar da ƙera makamin ƙare dangi

https://p.dw.com/p/137BN
Shugaban ƙasar Iran Mahmoud Ahmadinejad, na ziyara wata cibiyar sarafa ƙarfen uranium da ke kusa da TehranHoto: AP

Hukumar samar da makamashi nukliya ta duniya ta baiyana fargaban ta dangane da shirin ƙasar Iran na nukliya wanda ta zargi ƙasar da yunƙurin ƙera makamin ƙare dangin,a cikin wani rahoton da hukumar ta baiyana ta ambato cewar ƙasar ta Iran ta ƙera wani makamin Atom da ka iya zama babbar barazana ga zaman lafiya a duniya.

Sai dai a halin da ake ciki ƙasar ta Iran na ci gaba da dagewa akan masayin ta na mallakar nukliyar domin amfanin fara fula,a cikin wani jawabi da ya yi shugaban ƙasar na Iran ya ce barazanar da Amurka da kuma Isara'ila ke yi wa ƙasar sa ba wani sabon abu ne kuma ya musunta zargin.Kuma gwamnatin ƙasar ta yi shelar ci-gaba da aiwatar da shirin du da rahoton da ta baiyana ,nan gaba ne hukumar za ta baiyana rahoton a hukumce.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman