1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton Hukumar Red Cross a game da Palestinu

November 16, 2006
https://p.dw.com/p/Bubr

Hukumar bada agaji ta ƙasa da ƙasa, wato Red Cross, ta bayyana rahoto, a game da matsanacin halin taɓarɓarewa matakan kiwon lahia, a Palestinu.

Binciken da hukumar Red Cross ta gudanar, ya gano cewar mafi yawan assibitocin ƙasar, na aiki kadaran- kadahan, cikin ƙarancin kayan aiki, da na ma´aikata.

Hukumar ta yi kira ga ƙasashen turai da Amurika, su cenza sallon siyasa a wannan yanki, ta hanyar bada tallafi kuɗaɗe ga hukumar Palestinawa.

Idan dai a na tune, wannan ƙasashe, sun katse bada taimako ga Palestinu, tun bayan nasara ƙungiyar Hamas, a zaɓen yan majalisun dokokin watan Janairu, na shekara da mu ke ciki.

Dakatar da wannan tallafi, tamkar kissan kai ne, a wannan ƙasa, da ba ta wata hanya, ta samar da kudaden shiga, illa taimako daga ketare inji rahoton Red Cross.