Rahoton Hukumar Majalisar Turai Akan hakkin Dan Adam | Siyasa | DW | 09.06.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rahoton Hukumar Majalisar Turai Akan hakkin Dan Adam

A cikin rahoton da ta bayar dangane da Jamus Hukumar Majalisar Turai akan hakkin dan-Adam, ko da yake ta ya ba da irin ci gaban da aka samu a kasar amma tayi gargadi a game da barazanar kyamar baki dake da yada yaduwa, musamman a gabacin kasar

Majalisar Turai a Strassburg

Majalisar Turai a Strassburg

Bisa sabanin yadda lamarin ya kasance a shekarun baya, a wannan karon kwararrun masana al’amuran hakkin dan-Adam na Hukumar Tarayyar Turai sun yi magana da wata murya mai sassauci a cikin rahoton da suka bayar dangane da halin da ake ciki a Jamus na kyamar baki da tashe-tashen hankula akan Yahudawa. A shekara ta 2001, ministan cikin gida Otto Schily ya nuna bacin ransa a game da suka da kakkausan harshe da hukumar tayi na cewar mahukunta na Jamus na sako-sako da matsalar kyamar baki da adawa da Yahudawa a kasar. Ita kanta majalisar Turai ba ta ji dadin kakkausan lafazin da aka yi amfani da shi a wancan rahoton ba. Amma a wannan karon bayan da hukumar mai bitar matsalolin wariya da kabilanci a nahiyar Turai ta samu cikakkiyar kafa ta bin bahasin lamarin sosai da sosai ta canza lafazinta a rahotonta na bana, wanda shi ne na uku da ta gabatar akan Jamus. To sai dai kuma duk da haka ta kara da yin nuni da cewar tilas ne kasar ta Jamus ta tashi tsaye wajen magance matsalolinta na wariya da kyamar baki da kuma adawa da Yahudawa, lamarin dake barazanar zama ruwan dare a duk fadin kasar. Matsalar dai ta fi shafar manema mafakar siyasa da Yahudawa da kuma ‚yan kabilun Roma da Sinti masu dabi’u irin shigen na filanin daji. Rahoton hukumar yayi nuni da karuwar da aka samu ga barazanar da ake wa Yahudawa ta wasiku da wayoyin tarho tsakanin shekara ta 2001 zuwa shekara ta 2003. Har yau Jamus tana fama da matsalar nan ta hare-hare akan baki da tsirarun kabilu, wadanda kan kai ga raunata ko kuma kisan mutanen da lamarin ya shafa. Kungiyoyi masu zaman kansu a kasar sun sha yi nuni da yadda masu ra’ayin Nazinhitler da masu kwaryan molo da ake kira Skinheads ke dada samun bunkasar ayyukansu, musamman ma a gabacin Jamus. Alkaluma sun nuna cewar a halin yanzu haka, wadannan masu kyamar baki da ra’ayin wariyar jinsi suna da dakaru kimanin dubu 10 dake cikin damara. Wani abin da ya taimaka wajen samun wannan mummunan ci gaba shi ne wata sabuwar dabi’ar da ta yadu tsakanin matasa akan wani salo na kida da wasu fina-finai na Video, wadanda ake amfani da su domin yayata akidar wariyar jinsi. Wannan dabi’ar tuni ta zaman ruwan dare tsakanin matasa a gabacin Jamus. A baya ga haka, tsiraru, musamman ma bakar fata, kan fuskanci muzantawa a hannun mahukunta, inda galibi akan ware su domin bincike a tashoshin jiragen kasa da filayen saukar jiragen sama. Kazalika, kamar yadda rahoton ya nunar, mata Musulmi da kan daura dan-kwali su kan fuskanci wariya da cin mutunci a wuraren aikinsu. Kwararrun masanan akan hakkin dan-Adam dake garin Straßburg sun yi kira ga gwamnati da tinkari matsalar ta hanyar tsawwala dokar hukunta wadanda aka samesu da laifukan keta haddin tsiraru bisa wata manufa ta wariyar jinsi. Sai dai kuma hukumar ta yaba da wasu sabbin matakai da gwamnati ta dauka, kamar dai sassauta wa bakin damar zama ‚yan kasa da aka yi da kuma tattaunawar da ake yi a game da wata sabuwar doka ta kaka-gida a Jamus.