Rahoton Hukumar ƙwadago ta ƙasa da ƙasa.
April 27, 2007Hukumar ƙwadago ta ƙasa da ƙasa, ta bayyana rahoto a game da matsanancin halin da yan ƙwadago ke gudanar da ayyuka a ƙasashe daban-daban na dunia.
Rahotonya nunar da cewa a ko wace shekara ma´aikata fiye da milion 2 ke rasa rayuka a sakamakon cuttukan da su ka ɗauka a lokacin aiki, kokuma a cikin haɗari wurin gudanar da ayyuka.
Wannan rahoto da hukumar ƙwadago ta bayyana, ya ƙara da cewa, a ko wace shekara ma´aikata milion ɗari 2 da 70, ke jin raunuka a bakin aiki.
Wannan al´amari na jawo assara mai tarin yawa ga ci gaba tattalin arzikin dunia.
Hukumar ta bada shawarwari ga kampanomni da masa´antu, a game da matakan rage abkuwar wannan haɗarruruka.
Baban mataki acewar ta shine gunadar da bincike na kayan aiki da lafiyar ma´aikata lokaci zuwa lokaci.