1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rahoton HRW a game da yankin Darfur

A wani rahoto da ta bayyana yau litinin ƙungiyar kare hakokin bani adama ta Human Right Watch, ta bayana matsananci hali, da al´umomi yankin Darfur na kasar Sudan ke fama a ciki.

Rahoton ya ce a halin yanzu, dubun dubatar mutane, na yankin, na cikin halin laha ula´i.

Human Rigth Watch, ta zargi gwamnatin Sudan da yan tawaye, da ƙara dagulla al´ammura a yankin,inda mutane fiye da dubu 650, ba su da damar, samun tallafin da kungiyoyjn kasa da kasa ke badawa, a dalili da hare haren da rundunonin ɓangarorin 2, ke kai wa ga motoci da jami´an kungiyoyin bada agaji.

Wannan rahoto,ya yi kira ga yan tawaye Darfur, da Gwammnatin Khartum, da kuma kasashen dunia, da su kara lunka kokari, domin ceton rayukan mutane million3 da ke zaune a yankin Darfur, wanda kuma kacokam !!! su ka yi dogaro da taimako domin rayuwa.

Ranar juma´ada ta gabata, a birnin Abuja na tarayya Nigeria, an rattaba hannu akan yarjejeniya tsakanin yan tawaye da gwamnatin Sudan, to saidai har yanzu ,da sauran rina kaba, ta la´akari da cewar, wasu daga ɓangarorin tawaye ba su sa hannu ba, akan wanan sulhu.